Ku fito da sunayen Malaman zabe nan da sa’a 48 – PDP ta fadawa INEC

Ku fito da sunayen Malaman zabe nan da sa’a 48 – PDP ta fadawa INEC

- PDP tana kukan cewa APC na shirin hada kai da INEC wajen murde zaben bana

- Jam’iyyar ta nemi INEC ta fitar da sunayen Turawan zaben da za ayi aiki da su

- Kola Ologbondiyan na Jam’iyyar PDP ya nemi Kasashen waje su sa ido kan INEC

Ku fito da sunayen Malaman zabe nan da sa’a 48 – PDP ta fadawa INEC

PDP na so a saki sunayen wadanda aka dauka aikin zabe a 2019
Source: UGC

Mun samu labari cewa babbar jam’iyyar hamayya ta Najeriya, PDP, ta nemi hukumar zabe na kasa mai zaman kan-ta watau INEC, ta fito da jerin sunayen Malaman zaben da za ayi aiki da su wajen gudanar da babban zaben bana.

Jam’iyyar adawar ta nemi INEC ta bayyana sunayen daukacin wadanda za su yi aikin zaben da za ayi kwanan nan a fadin Najeriya. PDP tayi wannan kira ne ta bakin Sakataren ta na yada labarai na kasa Mista Kola Ologbondiyan.

KU KARANTA: An maka wani babban Ministan Najeriya a gaban Kotu a Legas

A jiya Litinin ne, Kola Ologbondiyan, ya bayyana cewa idan har hukumar zabe na INEC ba ta bayyanawa Duniya sunayen wadanda ta dauka su yi mata aikin zabe a Najeriya ba, babu shakka akwai gaskiyar shirin murde zaben.

Sakataren yada labaran na PDP yana zargin hukumar INEC da neman murde zabe domin Muhammadu Buhari ya sake samun nasara a zaben da za a yi a tsakiyar watan nan. INEC dai ta sake musanya irin wannan zargi na PDP.

PDP tayi kira ga kasashen waje su zura idanu a kan shugaban INEC da manyan jami’an hukumar wajen ganin ba a tafka magudi domin jam’iyyar APC mai mulki ta lashe zaben da za a yi a Najeriya ba.

Idan ka na da wata shawara ko bukatar ba mu labari, a tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Ku same mu a https://www.facebook.com/legitnghausa

Ko a http://twitter.com/legitnghausa

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta LEGIT NG Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Shafin NAIJ Hausa ya koma LEGIT

Source: Hausa.legit.ng

Mailfire view pixel