Yan majalisa sun kamala aiki akan sabon kudin dokokin zabe, duba muhimman dokoki 5 daga cikinsu

Yan majalisa sun kamala aiki akan sabon kudin dokokin zabe, duba muhimman dokoki 5 daga cikinsu

A ranar Talata 23 ga watan Oktoba ne majalisar dattawa ta kamala aiki akan sabuwar kundin dokokin zaben da take fata shugaban kasa Muhammadu Buhari zai rattafa hannunsa akansu don hukumar zabe mai zaman kanta ta kasa INEC ta aiwatar dasu.

LEGIT.com ta ruwaito Sanata Nazif Suleiman ne ya mika ma majalisar cikakken kwaskawararren dokokin, wanda a baya shugaba Buhari yayi watsi dasu, inda yace majalisar ta yi coge akan wasu muhimman abubuwa a wajen shirya dokokin.

KU KARANTA: An ji kunya: Wani Uba ya zakke ma diyarsa mai shekarau 16 har sai da ta mutu

A zaman majalisar na ranar Talata, shugabanta, Sanata Bukola Saraki ya yi kira ga kwamitin gyaran dokokin da ta tabbata ta bada kulawa ga dukkanin korafe korafen da shugaba Buhari yayi a baya, amma nan take Sanata Nazif ya amsa da cewa sun kula da bukatun shugaban.

Yan majalisa sun kamala aiki akan sabon kudin dokokin zabe, duba muhimman dokoki 5 daga cikinsu
Majalisa
Asali: Depositphotos

Daga cikin muhimman tanade tanade na kwaskwararren kundin dokokin zaben akwai;

Na’urar tantance masu kada kuri’a;

Doka na 14 daga cikin kundin dokokin zaben ya bayyana cewa “ A inda na’urar tantance masu kara kuri’a ya samu mastala a akwatin zabe, kuma ba’a samu wani na’ura ba har bayan awanni uku, ba za’ayi zaben ba, sai dai a daga shi a sanya lokacin yin sa a cikin awanni 24….”

Ranar kamamla zaben fidda gwani;

Doka na 24 dake sashi na 87 (1) ya warware matsalar dake tattare da zaben cikin gida, inda yace “Ranar zaben fidda gwani na jam’iyyu ba zai wuce kwanaki 150 kafin ranar babban zabe ba, ko yayi kasa da kwanaki 90 kafin ranar zaben.”

Tanadi game da cire alamar jam’iyya ko dan takara;

Doka na 32 dake sashi na 140 (4) ya warware rikicin dake biyo baya idan wata jam’iyya ta rasa alamar hotonta a takardar kuri’a ko sunan dan takararta, inda tace idan har haka ta faru, dokar ta bukaci jam’iyyar ko dan takarar daya sanar da hukumar zabe, inda za ta gyara matsalar, sa’annan ta shirya sabon zabe a cikin kwanaki 90.

Adadin kudin kashewa a yakin neman zabe;

Kudin dokar ta sanya adadin kudaden da doka ta amince kowanne dan takara zai iya kashewa a yayin yakin neman zabe; Shugaban kasa naira biliyan 5, Gwamna naira biliyan 1, Sanata naira miliyan 250, da Dan majalisar tarayya naira miliyan 150.

A yanzu dai ana jiran majalisar ta mika dokar ga shugaban kasa Muhammadu Buharo domin ya rattafa hannun a akanta.

Ku biyo mu a https://facebook.com/legitnghausa

ko a http://twitter.com/legitcomhausa

KU LATSA: Hanyar sauko da sabuwar manhajar jaridar Legit.com Hausa cikin sauki

Ga masu shawara ko korafi, a same mu a labaranhausa@corp.legit.com

Asali: Legit.ng

Authors:
Mudathir Ishaq avatar

Mudathir Ishaq Mudathir Ishaq is the head of the Hausa desk at Legit.ng. He studied Industrial Chemistry as first degree at the University of Abuja, Journalism (CSR Specialization) with the Michigan State University and runs MSc Industrial Chemistry from the Nasarawa State University, Keffi. With more than a decade experience in news reporting and content editing, he has interviewed influential personalities. He can be reached on: mudathir.ishaq@corp.legit.ng