Ba zan taba yarda ayi ma Buhari hawan kawara a majalisar dattawa ba – Inji Sanata

Ba zan taba yarda ayi ma Buhari hawan kawara a majalisar dattawa ba – Inji Sanata

Sanatan Solomon Adeola na jam’iyyar APC daga jahar Legas ya gargadi takwarorinsa Sanatoci dasu shiga taitayinsu kuma kada su kuskura su fara shirin yi ma shugaban kasa Muhammadu Buhari hawan kawara a majalisar ta hanyar rinjayarsa game da kudurin garambawul ga dokokin zabe.

Majiyar Legit.com ta ruwaito Sanatan ya bayyana haka ne cikin wata sanarwa daya fitar ta bakin kaakakinsa, Kayode Odunaro a babban birnin tarayya Abuja, inda yace ba zai zura wasu yan tsirarun Sanatoci su nemi yi ma shugaban kasa zagon kasa ba.

KU KARANTA: Wata sabuwa: Tazurai zasu fara biyan harajin rashin yin aure da wuri

Ba zan taba yarda ayi ma Buhari hawan kawara a majalisar dattawa ba – Inji Sanata
Sanata Solomon Adeola
Asali: UGC

Wannan magana ta biyo bayan kin amincewa da shugaban kasa Buhari yayi na rattafa hannu kan kudurin garambawul ga dokokin zabe da majalisun dokokin Najeriya suka yi ne, inda yace ba zai sa hannu akan kudurin don ta zama doka ba a yanzu da zabe bai wuce yan satuttuka ba.

Kin rattafa hannun da Buhari yayi ne yasa yan majalisun suka bayyana bacin ransu, inda suka dauki alwashin tattara yayan majalisun don ganin sun rinjayi shugaban kasa ta yadda idan har sanatoci kasha biyu bisa uku suka amince zasu rinjayi shugaban kasa kuma kudurin ta zama doka.

Da yake jawabinsa, Sanata Solomon yace duk masu kiran ayi ma Buhari hawan kawara basu da kyakkayar manufa ga Najeriya, basu kaunar ganin zaben 2019 ya samu nasara, a cewarsa matakin da Buhari ya dauka yayi daidai.

“A matsayina na Sanata kuma dan Najeriya ba zan shiga cikin masu kokarin rinjayar Buhari a majalisa dattawa akan kudurin dokokin zabe ba, asali ma zan yaki duk wani kokarin da aka yi makamancin haka a majalisar.

“Shugaban kasa ya bayyana dalilansa na kin rattafa hannu akan dokar, kuma ina ganin suna da karfin da kowa zai iya karbarsu, tunda dai ba wai yace ba zai sa hannu akan dokar bane, kawai cewa yayi bai dace dokar ta fara aiki a zaben 2019 ba.” Inji shi.

Ku biyo mu a https://facebook.com/legitnghausa

ko a http://twitter.com/legitcomhausa

KU LATSA: Hanyar sauko da sabuwar manhajar jaridar Legit.com Hausa cikin sauki

Ga masu shawara ko korafi, a same mu a labaranhausa@corp.legit.com

Sanarwa na musamman: Shafin NAIJ Hausa ya koma Legit Hausa

Asali: Legit.ng

Authors:
Mudathir Ishaq avatar

Mudathir Ishaq Mudathir Ishaq is the head of the Hausa desk at Legit.ng. He studied Industrial Chemistry as first degree at the University of Abuja, Journalism (CSR Specialization) with the Michigan State University and runs MSc Industrial Chemistry from the Nasarawa State University, Keffi. With more than a decade experience in news reporting and content editing, he has interviewed influential personalities. He can be reached on: mudathir.ishaq@corp.legit.ng