2019: Za ayi zabe na keke-da-keke a Najeriya inji Shugaban INEC

2019: Za ayi zabe na keke-da-keke a Najeriya inji Shugaban INEC

- Hukumar INEC tace za tayi gaskiya a zaben da za ta shirya a 2019

- Shugaban Hukumar yace za a hana amfani da waya wurin kada kuri’a

- Za kuma a karbe katin zabe daga hannun wadanda ba ‘Yan kasa ba

2019: Za ayi zabe na keke-da-keke a Najeriya inji Shugaban INEC

Hukumar INEC za ta hana sayen kuri'u a zaben 2019 inji Shugaban Hukumar
Source: Depositphotos

Hukumar zabe na kasa wtaau INEC ta bayyana cewa a shirye ta ke ta hada kai da Jami’an tsaro da sauran Hukumomi domin magance matsalar sayen kuri’u. Wannan matsala na sayen kuri’u yana ci wa Hukumar zaben tuwo a kwarya.

Shugaban Hukumar INEC na kasa, Farfesa Mahmood Yakubu, ya zanta da wasu gungun Matasa da fitattun Taurarin Kasar a Ranar Asabar dinnan da ta wue a Garin Legas inda ya bayyana cewa INEC za ta hana sayen kuri’u a zaben 2019.

Mahmood Yakubu yace za a haramta amfani da wayar salula a wurin dangwala kuri’a domin takawa masu sayen kuri’un jama’a burki. Yakubu dai ya bayyana cewa hukumar zaben za tayi kokari wajen ganin an yi adalci a zabe mai zuwa.

KU KARANTA: Tinubu ya jawo matsala a Jam’iyyar APC – Inji Sanatan PDP

Farfesa Yakubu ya kuma nuna cewa akwai wasu wadanda ba ‘Yan Najeriya bane da ke dauke da katin PVC kuma su ke shirin yin zabe a badi. Mahmud Yakubu yace za ayi amfani da Hukumar lura da shige da fice na kasar wajen taka masu burki.

Hukumar ta kuma tabbatar da cewa ko da Shugaba Buhari bai sa hannu kan sabon kudirin zabe ba, za a yi adalci a 2019 saboda irin matakan da aka dauka na amfani da na’urori na zamani kuma za a rika bayyana sakamakon zaben kowani akwati.

Hukumomin EFCC da ICPC masu yaki da barayi a Najeriya sun ce za su idanu a zaben 2019 domin ganin irin kudin da ‘Yan takara su ke kashewa. Sai dai kuma wasu manyan Lauyoyin Kasar sun fara nuna rashin gamsuwar su da wannan tsarin.

-

.

Idan ka na da wata shawara ko bukatar ba mu labari, a tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Ku same mu a https://www.facebook.com/legitnghausa

Ko a http://twitter.com/legitnghausa

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta LEGIT NG Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Shafin NAIJ Hausa ya koma LEGIT

Source: Legit

Mailfire view pixel