Hotunan Aure
Wata shahararriyar ‘yar tiktok Sarah Idaji Ojone ta shawarci maza su daina dauko batun aure idan sun san asusunsu bai cika taf da kudi ba, ta ce su ajiye N50m.
Wata kotu dake zamanta a Koriya ta kudu ta umarci shugaban rukunin kamfanonin SK, Chey Tae-won ya biya tsohuwar matarsa Roh So-young won tiriliyan 1.38.
Asirin wata amarya ya tonu a lokacin da aka je daukar hoton kafin aure, inda wanda za ta aura ya gano ta yi ciko a mazaunanta. A karshe dai ango ya fasa wannan aure.
Akwai tarin al'adu da dama a ƙasashen duniya wanda ya bambanta da saura, wasu kasashe sun amince da tsarin mata su biya maza sadaki yayin da suke neman aure.
Gwamnan jihar Kano, Abba Kabir Yusuf ta rattaba hannu kan dokar tilasta gwaji kafin aure domin kare yara daga cutukan da za a iya daukar matakan kariya a kansu.
Majalisar dokokin jihar Kano ta amince da kafa dokar gwajin lafiya kafin aure a fadin jihar. A jiya Litinin ne majalisar ta gama karanta kudurin dokar
A cikin faifan bidiyon, amaryar ta durkusa tana kokarin sumbatar ango amma ya rika zulle mata. Wannan ya jawo cece kuce ga mahalarta taron da 'yan soshiyar midiya.
Wani bidiyo da aka wallafa a yanar gizo wanda ya jawo magana ya nuna yadda wani dangi suka hadawa 'yarsu kayan alatu a ranar aurenta, wasu na ganin al'ada ce.
Matar da tasa a roƙi mijinta ya mayar da ita a Tafsirin 23 ga wata ya mayar da ita, Jabir Sani Maihula yayi jan hankali zuwa gare ta jiya bayan kammala Muhadara.
Hotunan Aure
Samu kari