An Gano Babban dalilin Buhari na Kin Amincewa Osinbajo Ya Fafata da Tinubu a 2023

An Gano Babban dalilin Buhari na Kin Amincewa Osinbajo Ya Fafata da Tinubu a 2023

  • Babachir Lawal ya ce marigayi Muhammadu Buhari na ganin bai dace Yemi Osinbajo ya fafata da Bola Tinubu ba
  • Tsohon sakataren gwamnatin tarayya ya bayyana cewa Buhari ya damu da naɗa mutanen Osinbajo, musamman waɗanda ake zargin ba su da ƙwarewa
  • Lawal ya ce Buhari ya amince da naɗe-naɗen ma’aikatan Osinbajo bayan ya duba takardar sunaye 28, inda ya yi wa mutum 26 alama da biro kore

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Abdullahi Abubakar, Editan Legit Hausa ne ta bangaren siyasa, kasuwanci da al'amuran yau da kullum, ya na da gogewar aikin jarida sama da shekaru biyar.

Abuja - Tsohon sakataren gwamnatin tarayya, Babachir Lawal, ya yi magana kan halayen tsohon shugaban kasa, Muhammadu Buhari.

Babachir ya ce marigayi Buhari na ganin matuƙar rashin ɗa'a ne kuma abin ƙyama Yemi Osinbajo, tsohon mataimakinsa, ya fafata da Bola Tinubu a zaɓen shugaban ƙasa na 2023.

Abin da ya sa Buhari ya bi Tinubu
Tsohon mataimakin shugaban kasa, Yemi Osinbaji da marigayi Muhammadu Buhari. Hoto: Muhammadu Buhari.
Source: Facebook

Hakan na cikin yake magana a wata hira da yan jaridu da TheCable ta bibiya inda ya ce zai yi wuya Buhari ya goyi bayan Osinbajo a kan Tinubu saboda dadaddiyar alaƙar da ke tsakaninsa da tsohon gwamnan Lagos.

Kara karanta wannan

Akwai dalili: Me yasa gwamnoni 33 ke goyon bayan tazarcen Tinibu?

Lawal ya ce matsayar Buhari ta samo asali ne daga biyayyarsa ga Tinubu, wanda ya bayyana a matsayin mutumin da ya ba Buhari shawarar tsayawa takarar shugaban ƙasa, sannan daga baya ya nemi ya gaje shi.

Ya ce:

“Na yi kusanci sosai da Buhari; na san shi sosai. Mutum ne da ya yi imani da biyayya. Yana kallon al'amura ta fuskar ɗabi'a da mutunci.”

A cewar Lawal, Buhari zai ɗauki matakin Osinbajo na ƙalubalantar Tinubu a takarar shugaban ƙasa a matsayin abin da bai dace ba, ba tare da la'akari da ra'ayinsa kan ƙwarewar tsohon mataimakin shugaban ƙasar ba.

“Buhari zai ga cewa babban rashin ɗa'a ne Osinbajo ya fafata da Bola Tinubu a takarar wannan muƙami,” in ji shi.

“Dangane da irin halinsa, zai ga hakan abin ƙyama ne saboda ya san alaƙar da ke tsakaninsu tun da farko; shi ne mutumin da ya ba shi shawarar tsayawa takarar shugaban ƙasa, kuma Bola yana son ya gaje shi.”

Kara karanta wannan

2027: Gwamna ya jawo wa mawaki Davido matsala da ya goyi bayan Tinubu

Lawal ya ƙara da cewa Buhari zai ga matakin Osinbajo a matsayin abin ƙyama “ko da yana ganin Osinbajo zai zama shugaban ƙasa mafi nagarta ko wani abu makamancin haka”.

Osinbajo, wanda ya riƙe muƙamin mukaddashin shugaban ƙasa a lokacin da Buhari ke tafiye-tafiyen neman magani a ƙasashen waje, ya ɗauki wasu matakai a lokacin da yake jagorantar ƙasar. Daga cikinsu akwai korar Lawal Daura, tsohon darakta-janar na Hukumar Tsaro ta Farin Kaya (DSS), a watan Agustan 2018.

Korawar ta biyo bayan mamayar da jami'an DSS suka yi wa harabar Majalisar Dokoki ta Ƙasa da ke Abuja, inda suka hana 'yan majalisa da sauran mutane shiga zaurukan majalisar.

Babachir ya yi magana kan Peter Obi

Mun ba ku labarin cewa Injiniya Babachir David Lawal yana ganin Peter Obi da Rabiu Kwankwaso ba su amfana da farin jininsu sosai.

Tsohon sakataren Gwamnatin tarayyan yana so ‘yan takaran na NDC su rika tallata kansu da kyau ga jam’a.

Idan sun shiga cikin jama’a, Babachir yana ganin da bukatar Obi da Kwankwaso su fadi manufofinsu da kyau.

Asali: Legit.ng

Authors:
Abdullahi Abubakar avatar

Abdullahi Abubakar (Hausa editor) Marubuci kuma kwararren ɗan jarida ne da ya shafe shekaru 5 yana rubutu a fannin siyasa da harkokin yau da kullum. Ya kammala digirin farko a jami'ar Maiduguri. Ya samu horon aikin jarida a Reuters da AFP, ya sha halartar tarukan karawa juna sani game da bincike da adabi. Tuntube shi a abdullahi.abubakar@corp.legit.ng.