NDC Tana Wani Fadan da INEC kan Ba Wasu Mutane daga Waje Tikitin Takara a Kano
- Jam’iyyar NDC a Kano ta zargi wata jami’ar INEC da fitar da rahotanni masu cin karo game da zaben tsaida gwani
- Ana kukan cewa rahotannin sun kunshi sunayen mutanen da ba su shiga zabn ba, aka ce su ne ‘yan takara a zaben 2027
- NDC ta bukaci INEC ta binciki lamarin, amma ba a samu martanin hukumar ko wata jami'a a Kano kan zarge-zargen ba
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Kano - Jam’iyyar NDC ta zargi Hukumar Zabe Mai Zaman Kanta ta Kasa (INEC) da kakaba mata wasu ‘yan takara.
NDC ta ce INEC ta fitar da rahotanni daban-daban masu sabani kan zaben fitar da gwanin jam’iyyar a reshen jihar Kano.

Source: Facebook
Kano: Jam'iyyar NDC ta kai kukan jami'ar INEC
Jam’iyyar ta yi wannan zargi ne a cikin wata takardar korafi mai kwanan wata 16 ga watan Oktoba, 2026 a cewar Daily Trust.
An shigar da korafi kan Hauwa Buhari Buhari, shugabar sashen zabe da sa ido kan jam’iyyun siyasa a ofishin INEC na Kano.
NDC ta aika da korafin ne ta hannun lauyoyinta, Tahir Chambers, zuwa ga INEC ta hannun Kwamishinan Zabe na jihar.
Jam’iyyar hamayyar ta yi zargin cewa jami’ar ta fitar kuma ta sanya hannu kan nau’ukan rahoto da dama masu karo da juna.
Ta ce rahoton zabukan fitar da gwani na jam’iyyar da aka samu daga wajen ta dauke da wasu bayanai masu sabani da juna.
NDC ta ce an cusa mata 'yan takara a Kano
Jam’iyyar ta ce wasu daga cikin rahotannin sun ambaci sunayen mutanen da ba ’yan takararta ba ne amma aka ba su tuta.
Ana zargin an dauko wasu da ba su da rajista kuma ba su shiga zabe ba, aka tsaida su a NDC.
A gefe guda, NDC ta yi korafin jami’ar INEC din ta cire sunayen wasu da jam’iyyar ta zaba bisa ka’ida domin wakiltar ta.
The Guardian ta ce NDC ta kuma nuna damuwa kan yadda ake yada rahotannin da ake takaddama a kansu a yanzu.
Wata matsalar da jam’iyyar ta nuna ita ce rashin bayyana ranar da aka gudanar da zaben tsaida gwanin cikin rahotannin.
Sannan jam’iyyar ta bukaci INEC ta lura da bambance-bambancen da ke cikin rahotannin.
Wani mataki NDC ta ke so a dauka?
Sai dai takardar korafin da aka samu ba ta fayyace duk matakan da take son hukumar ta dauka dangane da zaben na 2027 ba.
Har zuwa lokacin da aka fitar da rahoton, ba a tabbatar da tabbaci ko rashin hakan dangane da zarge-zargen da NDC ta yi ba.
Haka kuma, INEC da jami’ar da aka ambata ba su mayar da martani kan batun ba zuwa yanzu.

Source: Facebook
Hamza Telan Mata ya fitar da takardun korafin a Facebook
Rigima tsakanin hadiman gwamnan Kano
Labari ya zo cewa Alhaji Salisu Yahaya Hotoro yana ganin 'yan SR da SSR ba su kare gwamnan Kano yadda ya kamata.
Shugaban kungiyar masu dauko rahoto ya maida wa shugaban matasan APC a jihar Kano amsa saboda ya taba mutuncinsu.
Amir Kima ya ce suna tare da Abba Gida Gida kuma ‘yan kungiyarsu ba su jin tsoron wani hadimi da asali ma bai nufin su da alheri.
Asali: Legit.ng

