Hajjin Bana
Kasar Saudiyya ta samar da wata manhaja ta musamman domin masu karatun Al-Kur'ani mai girma. Sheikh Sudais ya ce mahajjata da sauran Musulmi za su amfana da ita.
Mataimakin shugaban ƙasa, Sanata Kashim Shettima ya jagoranci kaddamar da fara jigilar mahajjata daga Najeriya zuwa ƙasar Saudiyya, jirgin farko ya tashi a Imo.
Musa Iliyasu Kwankwaso ya yi zargin ana kokarin dagula harkokin hukumar alhazai ta NAHCON da bata sunan shugabanta, Farfesa Abdullahi Sale Usman Pakistan.
Hukumar kula da Alhazai ta Kwara ta ce za a fara jigilar farko ta alhazan a ranar 12 ga Mayu, yayin da ta ce an tanadi masauki da abinci har zuwa karshen Hajji.
Hukumar alhazai ta kasa ta sanar da cewa a ranar 9 ga Mayu mahajjatan Najeriya za su fara tashi daga Najeriya zuwa Saudiyya domin aikin hajjin 2025.
Mataimakin Shugaban Ƙasa, Kashim Shettima, ya tura sakon gayyata ga shugaban NAHCON, Farfesa Abdullahi Saleh Pakistan da mambobin kwamitinsa domin taro a Abuja.
Kashim Shettima ya ja kunnen shugaban NAHCON, Farfesa Usman, da ya dakatar da gudanar da hukumar shi kaɗai tare da sanya kwamishinonin hukumar a harkokin gudanarwa.
Saudiyya ta saka 29 ga Afrilu a matsayin ranar ƙarshe da maniyyatan Umrah za su bar ƙasar. Wanda ya karya dokar zai fuskanci hukuncin tara da daurin watanni.
Kwamishinonin NAHCON sun zargi shugaban hukumar da karya dokoki da ware su daga ayyuka, sun kuma aike da takardar koke zuwa ofishin mataimakin shugaban kasa.
Hajjin Bana
Samu kari