Wahalar man fetur a Najeriya
Gwamnatin tarayya ta fadi dalilin shigo da man fetur daga kasashen ketare duk da cewa matatar man Dangote da ke Legas ta fara aiki, Hukumar NMDPRA ta yi bayani.
Mambobin kungiyar dillalan man fetur mai zaman kanta ta Najeriya da kungiyar ma’aikatan man fetur da iskar gas a jihohin Oyo da Osun sun rufe gidajen mansu.
Dillalan man fetur a Najeriya sun bayyana hanyar da za a bi don tabbatar da man fetur ya sauka gaba daya. Sun ce, ya kamata a ware masu kaso 50% na man kasar.
A lokacin da 'yan Najeriya ke fama da dawowar layukan mai, hukumar kwastam ta cafke wasu dauke da fetur da za a yi safararsa zuwa kasar Kamaru ta iyakar kasar nan.
Mele Kyari, shugaban kamfanin NNPC, ya ce kamfanin ya fara tattaunawa domin karbo sabon rancen kudi wanda zai yi amfani da su wajen tafiyar da ayyukansa.
Kamfanin man fetur na Najeriya, NNPCL, ya bayyana cewa ambaliyar ruwa da matsalar sufuri ce ta assasa karuwar layikan mai a babban birnin tarayya da wasu jihohi.
Kamar yadda Alhaji Aliko Ɗangote ya bayyana a baya, matatar da ya gina mai karfin ta ce gangar mai 650,000 ta jaddada fara shigo man fetur kasuwa a watan Yuli.
Kungiyar 'yan kasuwa ta makamashin man fetur ta kasa (MEMAN) ta bayyana dalilin da ya sa aka samu karancin shigo da mai, inda ya ta ce mamakon ruwa ne ya jawo.
An shiga fargabar dawowar matsalar man fetur Najeriya bayan an gano kamfanin man fetur na kasa (NNPCL) ya fada matsalar bashi, yayin da ya gaza biyan $6bn.
Wahalar man fetur a Najeriya
Samu kari