Wahalar Fetur Ta Tsananta a Najeriya, NNPC Zai Nemo Sabon Rancen Dala Biliyan 2

Wahalar Fetur Ta Tsananta a Najeriya, NNPC Zai Nemo Sabon Rancen Dala Biliyan 2

  • Rahotanni sun bayyana cewa kamfanin NNPC ya fara shirin karbo sabon bashin $2bn da zai bashi damar tafiyar da ayyukansa
  • An ce basusukan da dillan mai ke bin kamfanin NNPC ya karu sosai a cikin watanni hudu da suka wuce inda ya kai dala biliyan 6
  • Wannan dai na zuwa ne yayin da wahalar fetur ta tsananta a Najeriya, inda NNPC ya fito ya fadi abin da ya jawo karancin man

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Sani Hamza, kwararren edita ne a fannin nishadi, al'amuran yau da kullum da kuma siyasa. Sani yana da shekaru sama da biyar a aikin jarida

Abuja - Kamfanin NNPC ya fara tattaunawa kan karbo wani sabon bashi da zai bashi damar tafiyar da ayyukansa, wanda zai biya daga man da ake hakowa.

Shugaban kamfanin, Mele Kyari ya bayyana hakan a yayin da rahotanni suka bayyana cewa NNPC na fuskantar matsin lamba sakamakon wahalar fetur ta tsananta.

Kara karanta wannan

Karancin albashi: Bayan ragi sau 3 NLC, TUC sun ta kafe kan N250,000

Mele Kyari ya yi magana kan shirin NNPC na karbo sabon bashi
NNPC ya sanar da shirinsa na karbo sabon bashi. Hoto: @nnpclimited
Asali: Facebook

NNPC na neman rancen $2bn

A tattaunawarsa da kafar labaran Reuters, Mele Kyari ya ce NNPC za ta karbi bashin ne a kan hako ganga 30,000-35,000 kowace rana amma bai fadi adadin da ake nema ba.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Sai dai wasu majiyoyi guda biyu da ke da masaniya kan lamarin sun bayyana cewa kamfanin NNPC yana neman akalla bashin dala biliyan biyu domin tafiyar da aikinsa.

A hannu daya kuma basusukan da dillan mai ke bin kamfanin NNPC ya karu sosai a cikin watanni hudu da suka wuce inda ya kai dala biliyan shida.

NNPC ya karyata rike kudin dillai

Jaridar The Punch ta ruwaito cewa Olufemi Soneye, mai magana da yawun NNPC ya karyata rahoton Reuters na cewa dillalan mai na bin kamfanin bashin dala biliyan shida.

“Ba gaskiya bane. Sun bayyana sunayen dillalan da suka yi ikirarin suna binmu bashi? Su fitar da sunayen idan gaskiya suke fada."

Kara karanta wannan

Ana tsaka da wahalar fetur, NNPCL ya fadi abin da ya jawo dogon layi a gidajen mai

Mele Kyari dai ya ce za su yi amfani da sabon bashin ne domin aiwatar da dukkanin harkokin kasuwanci na NNPC, ciki har da tallafawa ci gaban hako mai.

NNPC ya yi magana kan wahalar fetur

A wani labarin, mun ruwaito cewa kamfanin man fetur na Najeriya, NNPC, ya sanar da dalilan da suka kawo karancin man fetur da ake fuskanta a sassan kasar nan.

NNPC ya ce an samu karancin fetur din ne sakamakon ambaliyar ruwan sama, tsaiko wajen dakon man da kuma matsalolin da ake samu yayin kai fetur din gidajen mai.

Asali: Legit.ng

Authors:
Sani Hamza avatar

Sani Hamza Sani Hamza ma'aikaci ne da ya yake da gogewa a aikin jarida. Ba fassara labarai da wallafasu a yanar gizo kadai ba, Sani yana da kwarewa a aikin rediyo da talabijin. Ya kuma shafe shekaru 8 a masana'antar fina-finai da dab'i.