Gwamnatin tarayyar Najeriya
Mataimakin shugaban ƙasa, Kashim Shettima, ya ƙaddamar da rabon buhunan taki sama da 515,000 ga manoma 128,930 domin ƙara yawan amfanin gona da tsaron abinci.
Kungiyar gwamnonin Najeriya (NGF) ta karbi bayanai tare da amince wa da kudirin kafa rundunar yan sandan jihohi yayin da tsaro ke kara tabarbarewa.
Yan majalisar wakilan tarayya na jam'iyyun adawa sun bukaci shugaban kasa, Bola Ahmed Tinubu ya jagoranci kasar nan yadda ya kamata ko ya yi murabus.
Gwamnatin tarayya ta ware kimanin N50m domin tallafa wa masu fama da cutar daji, inda za a ba kowane wanda ya cancanta akalla tallafin Naira 100,000.
Ma'aikatar kudi ta tarayya ta musanta labarin cewa gwamnatin Tinubu na shirin dora karin haraji a harkokin sadarwa da man fetur, ta ce labarin ba gaskiya ba ne.
Kungiyoyin NLC da TUC sun sanar da shirin fara tattaunawa da gwamnatin tarayya kan sabon mafi karancin albashi, saboda hauhawar farashi da ta yi wa ma’aikata katutu.
Masu zanga-zanga kan tabarbrewar tsaron Najeriya sun sake fitowa a rana ta uku a Abuja, sun toshe titin Karu-Nyanya domin jawo hankalin gwamnatin tarayya.
Karamin ministan tsaro, Muhammad Bello Matawalle ya bayyana cewa yan adwa na amfani da halin da ake ciki na rashin tsaro wajen tunzura yan Najeriya.
Ministan tsaron Najeriya, Janar Chirstopher Musa (Mai ritaya) ya bukaci yan Najeriya su hada kai su taimaka wa jami'an tsaro don dawo da zaman lafiya.
Gwamnatin tarayyar Najeriya
Samu kari