Gwamnatin Najeriya
Gwamnatin tarayya ta hannun ma’aikatar ayyuka za ta kawo sabon tsarin karbar haraji a kan titin Abuja zuwa Keffi da mayar da Keffi-Akwanga-Markurdi zuwa hannu biyu.
Hawaye da firgici sun mamaye wasu mazauna Abuja yayin da hukumar FCTA karkashin jagorancin Nyesom Wike ta fara rusa wasu gine-gine a ranar Alhamis.
Dakta Isa Yuguda, tsohon gwamnan jihar Bauchi, ya bayyana cewa Gwamnatin shugaba Bola Tinubu ta fara magance matsalar wutar lantarki da ta gaggari gwamnatocin baya.
Mashawarcin shugaban kasa a kan harkokin tsaro, Nuhu Ribadu ya zargi cewa mafi yawan makaman da ke yawo a hannun bata-garin mutane a kasar nan mallakin gwamnati ne.
Gwamnatin tarayya ta gargadi mutanen jihohi kan samuwar ambaliyar ruwa. Gwamnatin ta ce za a iya samun mummunar ambaliya a Kogi, Taraba, Neja da Benue.
Gwamnatin Bola Tinubu ta yi wa yan kwadago sababbin alkawura kan karin kudin fetur. Gwamnatin Najeriya ta ce za ta tabbatar an yi karin albashi a dukkan jihohi.
Mataimakin shugaban kasa Sanata Kashim Shettima ya isa Sweden domin wakiltar Bola Ahmed Tinubu. Kashim Shettima zai tattauna ne kan harkokin kasuwanci.
Gwamnatin Bola Ahmed Tinubu ta ce a cikin wasu shekarar 2023, za ta fitar da jama'ar kasar nan akalla miliyan 100 daga kangin talauci da ake ciki a yanzu.
Bayan tafiyar Tinubu hutu an yi jita jitar cewa Tinubu ba shi da lafiya yana asibiti, an kara kudin fetur kuma an yawaita kiran Tinubu da T-Pain ciki har da Atiku.
Gwamnatin Najeriya
Samu kari