Gwamnoni Za Su Yi Bushaha, Tinubu Zai Aikawa Jihohi 36 Naira Tiriliyan 1

Gwamnoni Za Su Yi Bushaha, Tinubu Zai Aikawa Jihohi 36 Naira Tiriliyan 1

  • Gwamnatin tarayya za ta cire Naira Tiriliyan 1 daga asusun ECA, ta rabawa jihohin Najeriya
  • Abin da ya faru shi ne Gwamnatocin jihohi sun gano an fitar da kudin da aka tara daga rarar mai
  • Dole ne gwamnatin Najeriya ta maidawa jihohi da kananan hukumomi hakkinsu daga cikin asusun

Abuja - Asusun jihohi zai cika da makudan kudi a sakamakon amincewa da gwamnatin tarayya ta yi na biyansu hakkokinsu daga ECA.

A wani rahoto da mu ka samu daga The Nation, an fahimci gwamnatin tarayya za ta maidawa gwamnatocin jihohi kudi Naira tiriliyan daya.

Wadannan makudan kudi sun wakilci kashi 25.6% na Naira Tiriliyan 3.9 da gwamnati ta cire daga asusun ECA ba da sanin jihohi ba.

Gwamnoni
Bola Tinubu tare da Gwamnoni Hoto: @DOlusegun
Asali: Twitter

Tarihin asusun ECA a Najeriya

A shekarar 2004, gwamnatin Olusegun Obasanjo ta kirkiri asusun na ECA domin a rika tara rarar kudin da aka samu a wajen saida mai.

Kara karanta wannan

Dan Najeriya Da Ke Tuka Baro a Kasuwa Ya Zama Shahararren Farfesa Da Ake Ji Da Shi

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Amfanin ECA shi ne a iya tara kudi a lokacin da ake cin kasuwar mai ta yadda za a tsira da dukiya idan farashin ganga ya karye a kasuwa.

Za a rika aika kudin sannu-sannu

Rahoton ya ce gwamnati ba za ta damkawa gwamnonin jihohi duka kudin a lokaci guda ba.

Za a rika cire Naira biliyan 50 ko Naira biliyan 100 ne a sannu a hankali daga asusun rarar man ana biyan jihohi, har a kammala biyansu.

Wata majiya daga ma’aikatar tattalin arziki ta ce gwamnatocin jihohi sun gano an taba kudin asusun, sai su ka tunkari gwamnatin tarayya.

Da maganar ta je Abuja, gwamnatin tarayya ta amince ta biya gwamnoni kasonsu na kudin da aka cire ba tare da an ankarar da jihohin ba.

Me gwamnati tayi da N3.9tr?

Majiyar ta ce an yi amfani da wasu daga cikin kudin wajen rage bashin da ake bin gwamnati ne.

Kara karanta wannan

Babu Wata Yarjejeniya Da Emefiele Kan Dawo da ‘Biliyan 50’, Gwamnatin Tinubu

Zuwa yanzu abin da ya rage a asusun bai wuce $473,754.57 ba. Idan kudi sun yi kasa zuwa Naira biliyan 650, doka ta hana a taba asusun.

Bola Tinubu v Atiku Abubakar

Ana da labari Alhaji Atiku Abubakar zai kinkimi takardun da ya samu daga jami’ar Amurka, ya tafi kotun koli domin kalubalantar Bola Tinubu.

‘Dan takaran shugaban kasar na PDP ya huro wuta sai an tunbuke Shugaba Tinubu daga kan mulki, ya na zargin cewa bai dace da takara ba.

Asali: Legit.ng

Authors:
Muhammad Malumfashi avatar

Muhammad Malumfashi (Hausa writer) M. Malumfashi ya samu Digirin farko a ilmin komfuta a ABU Zaria. Baya ga haka ya yi Digirgir a fannin kula da bayanai da wani Digirgir a ilmin aikin jarida duk daga jami'ar. Malumfashi ya kan kawo labaran siyasa, addini, wasanni da al’ada. Ya halarci taron karawa juna sani iri-iri. Imel: muhammad.malumfashi@corp.legit.ng

Online view pixel