Labaran Kwallo
Da yake amfani da gogewa a harkar fina-finai, talabijin, kiɗa, da ƙwallon ƙafa, ɗan fim ɗin ya ce ya kulla jarjejeniya da gwamnatin Katsina domin horar da matasa.
Gwamnan jihar Kano, Abba Kabir Yusuf ya nada Ahmed Musa mukami a gwamnatinsa. Gwamna Abba ya nada Ahmed Musa mukamin jakadan wasanni na jihar Kano.
'Yan wasan Kano Pillars (U-19) sun yi hatsarin mota a kan hanyarsu ta zuwa sabon filin wasanni na Jos. An ce direban motar da 'yan wasa da dama sun jikkata.
OJB Media Network ta karrama Mai girma gwamnan Katsina, Malam Dikƙo Umaru Radda da lambar yabon ƙasa da kasa kan gudummuwarsa a bangaren wasanni.
Rahotanni sun bayyana cewa Dan wasan Najeriya Victor Boniface ya tsallake rijiya da baya a wani mummunan hatsarin mota da ya rutsa da shi a kasar Jamus.
Za a ji yadda aka yaudari Barcelona, aka damfare ta €1m wajen sayen Lewandowski. Yayin da ake kokarin sayo Robert Lewandowski daga Jamus, an yaudari Barcelona.
'Yan wasan kwallon kafa na Najeriya watau Super Eagles sun dawo gida Najeriya bayan 'wulakanta' su a filin jirgin Libya, sun dawo ba tare da buga wasa ba.
Yan kwallon Najeriya sun makale a filin jirgin saman Libya yayin da za su buga wasa. Libya ta ce matsalar sufuri ce ta jawo kuma su ma sun samu matsala a Najeriya.
Rahotanni sun ce hukumomin Spain sun kama dan wasan Manchester City da Portugal, Matheus Nunes a farkon watan Satumba bisa zargin satar wayar salula.
Labaran Kwallo
Samu kari