Zaben Shugaban kasan Najeriya
An samu wasu fusatattun matan da suka shirya zanga-zanga a ofishin Jakadancin Amurka. Wadannan mata sun nuna ba su ji dadin abin da ya faru a zaben 2023 ba.
Farfesa Gideon Christian ya roki ICC ta yi bincike a kan irin abubuwan da Bayo Onanuga ya fada. Takardar da ya aikawa kotun Duniya ya isa Hague a makon nan.
Ana kokarin fatattakar Shugaban Jam’iyyar PDP na kasa, Sanata Iyorchia Ayu daga ofishinsa. Abubuwan sun cabe a sakamakon majalisar NWC da ta ladabtar da wasu.
Akwai mutane kusan 10 da ba za su iya samun bizar shiga Ingila ba saboda bakinsu. Kalaman da wadannan 'yan siyasa su ka rika yi su na da hadari ga damukaradiyya
Peter Obi, dan takarar shugaban kasa na jam'iyyar Labour a zaben 2023 da takwararsa na PDP, Atiku Abubakar sun tafi kotu don kallubalantar nasarar Tinubu na APC
Dan majalisar tarayya mai wakiltan mazabar Ikwo/Ezza ta kudu, Kwamrad Chinedu Ogah (OON), ya bayyana cewa shugaban INEC ya ciri tuta kan gudanarwar zaben 2023.
Tarihi ya nuna cewa galibi shugabannin Najeriya da ke kan mulki ba su cin akwatunan zabe da ke fadar shugaban kasa wato Aso Rock duk da kasancewarsu kan mulki.
Atiku Abubakar, dan takarar shugaban kasa na jam'iyyar PDP a zaben ranar 25 ga watan Fabrairu ya musanta janye kararsa na kallubalantar nasarar Bola Tinubu.
Za a ji a makon gobe ne ‘Yan takaran da suka yi nasara a zaben Majalisa za su samu satifiket a jihohinsu, haka abin yake ga zababbun Gwamnoni da mataimakansu.
Zaben Shugaban kasan Najeriya
Samu kari