Zaben Shugaban kasan Najeriya
Gwamnan jihar Nasarawa, Abdullahi Sule, ya yi magana kan zaben shugaban kasa na shekarar 2027. Gwamnan ya ce yankin Arewa zai sake goyon bayan Shugaba Bola Tiinubu.
Babban kusa a jam'iyyar NNPP mai adawa a Najeriya, Buba Galadima, ya bayyana cewa dole ne 'yan Najeriya su tashi tsaye domin ganin an yi zabe na gaskiya a 2027.
Gwamna Umo Eno na jihar Akwa Ibom ya bayyana cewa ko kaɗan bai ci amanar PDP don bayyana shirinsa na marawa shugaban kasa, Bola Tinubu baya a 2027.
Tsohon ɗan takarar mataimakin shugaban kasa a inuwar LP, Yusuf Datti Baba Ahmed ya ce alamu sun nuna APC ba za ta kai labari ba, ya shawarci Tinubu ya hakura.
An yada wasu rahotanni masu cewa Goodluck Jonathan ya yi hasashen nasarar shugaban kasa Bola Ahmed Tinubu a zaben 2027. An gano gaskiya kan batun.
Tsohon ɗan Majalisar wakilan tarayya, Hon. Farouk Aliyu ya bayyana cewa da iƙon Allah shugaban ƙasa, Bola Ahmed Tinubu zai yi takwas a kan madafun iko.
Gwamna Seyi Makinde na jihar Oyo ya bayyana cewa duk da bai kai ga yanke shawara ba amma yana da kwarewa da cancantar zama shugaban kasa a Najeriya.
Dan gwamnan Bauchi, Injiniya Bala Mohammed ya yi zargin cewa Atiku Abubakar da yi wa mahaifinsa bakin cikin zama gwamnan jihar a zaben 2023 da ya gabata.
Shugaban hukumar INEC, Mahmood Yakubu ya bayar da tabbacin cewa wa'adinsa a matsayin shugaban hukumar zaben ya zo karshe, kuma zai ajiye aiki a karshen shekara.
Zaben Shugaban kasan Najeriya
Samu kari