Jam'iyyar APC
Gwamnan jihar Adamawa, Ahmadu Umaru Fintiri ya umarci jami'an da ya ba mukaman siyasa da su koma jam'iyyar APC cikin sa'o'i 48 ko ya kore su daga aiki.
A labarin nan, za a ji cewa wasu daga cikin yan APC reshen jihar Legas sun zargi jam'iyyar da rashin gaskiya game da zaben fitar da gwani da aka yi.
A labarin nan, za a ji cewa daya daga cikin manyan 'yan jam'iyyar APC a Kano, Fa'izu Alfindiki ya ce lokaci ya yi da Sanat Rabiu Musa Kwankwaso zai bar NDC.
Shugabannin APC a mazabar Pantami da ke karamar hukumar Gombe aun ce ba su damsaniyar Isa Pantami ya bar jam'iyyar kafin ya shiga PDP har a ba shi takara.
Jam'iyyar APC ta rasa wasu daga cikin mambobinta bayan ta gudanar da zabubbukan fitar da gwani. Tsofaffin shugabannin majalisa na cikin wadanda suka fice.
Sanata Ali Muhammad Ndume ya ce akwai bukatar jam'iyyar APC ta kara kaimi wajen hada kan jama'a idan tana son cin zaben shekarar 20027 da ke tafe.
Iyabo Obasanjo, diyar Olusegun Obasanjo ta yi murabus daga APC a Ogun bayan ta zargi shugabannin jam’iyyar da nuna mata rashin adalci a zaben fidda gwani.
Tsohon sakataren gwamnatin tarayya (SGF), Babachir Lawal, ya bayyana cewa wasu gwamnonin jam'iyyar APC na zawarcinsa domin ya koma cikinta biyo bayan barin ADC.
Sakataren jam'iyyar ADC, Dr Ahmad Gana, dan takarar majalisar wakilai, Muhammad A Bello da dan takarar majalisar jihar, Mubarak Musa Dantori sun oma PDP da APC.
Jam'iyyar APC
Samu kari