Jihar Benue
Jami'an yan sanda sun yi kokarin tarwatsa wasu da ake zaton magoya bayan Gwamna Alia ne yayin da suka yi yunkurin taɗa rikici a sakatariyar APC a Makurdi.
Hukumar ƴan sanda reshen jihar Benuwai ta kwace iko da babbar sakatariyar APC mai mulki a jihar bisa umarnin Gwamna Alia na hana duk wani taron siyasa.
Rundunar 'yan sandan jihar Benue ta samu nasarar cafke wasu masu kera makamai a jihar. Rundunar ta cafke miyagun ne bayan samun bayanan sirri kan ayyukansu.
Gwamna Hyacinth Alia na jihar Benuwai ya kaddamar da kwamitocin da zasu gudanar da bincike kan yadda aka yi hada-hadar kuɗin al'umma a shekaru 8 na Ortom.
Tsohon gwamnan jihar Benuwai, Samuel Ortom, ya bayyana cewa ba inda za shi, yana nan a matsayinsa na jagoran PDP na jihar Benuwai amma ba shi da shirin shiga APC.
Majalisar tsaro ta jihar Benuwe ta baiwa makiyaya wa'adin kwanaki 14 da su daina kiwon dabbobi a fili ko kuma su fuskanci hukunci kamar yadda dokar jihar ta tanadar.
Dan majalisar tarayya mai wakiltar mazabar Ado, Okpokwu, da Ogbadibo a jihar Benue, Philip Agbese, ya soke bikin zagayowar ranar haihuwarsa saboda tsadar rayuwa.
Wasu miyagun 'yan bindiga dauke da makamai sun kai sabon hari a jihar Benue inda suka tafka mummunar ta'asa. 'Yan bindigan sun salwantar da rai tare da kona gidaje.
Wasu tsagerun mahara da ake kyautata zaton fulani makiyaya ne sun halaka rayukan mutane 10 a wasu hare-hare da suka kai lokaci guda a kauyuka 5 a jihar Benue.
Jihar Benue
Samu kari