Sata Kirikiri: Yadda Aka Kwamushe Ma’aikatan Banki 2 da Zargin Sace Kudi a Asusun Mamaci

Sata Kirikiri: Yadda Aka Kwamushe Ma’aikatan Banki 2 da Zargin Sace Kudi a Asusun Mamaci

  • An kwamushe wasu ma’aikatan bankin da ake zargin sun cinye kudin mamaci a daidai lokacin da danginsa ke neman sauran abin da ya bari
  • An gano yadda ma’aikatan bankin biyu suka hada baki tare da sace kudin mutumin da ya yi ajiya a bankin na tsawon lokaci
  • Ba sabon abu bane samun ma’aikatan gwamnati da na kamfanoni masu zaman kansu su saci kudi, hakan ba zai rasa nasaba da son zuciya ba

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Salisu Ibrahim ne babban editan sashen Hausa na Legit. Kwararren marubucin fasaha, harkar kudi da al'amuran yau da kullum ne, yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru takwas

Makurdi, Benue - Jami’an hukumar yaki da cin hanci da rashawa ta EFCC reshen Makurdi sun kama wasu tsoffin ma’aikatan banki a birnin bias zargin satar N4,199,500 mallakin wani kwastoman da ya rasu.

Kara karanta wannan

Wuce gona da irin Isra'ila: Isra'ila ta farmaki makarantar majalisar dinkin duniya a Gaza

An kama wadanda ake zargi, Idah Ogoh da Agbo Okwute, a ranar Jumma’a, 21 ga Yuni, 2024 a garin Makurdi, Jihar Benue.

Jami'an EFCC sun kame ma'aikatan banki da sace kudin kwastoma
Yadda aka kama ma'aikatan banki da sace kudin kwastoma | Hoto: Economic and Financial Crimes Commission (EFCC)
Asali: Facebook

Kwamushe su ya biyo bayan korafin da bankin ya shigar a kansu bisa zargin cirar kudi daga asusun marigayin, Emmanuel Azer Agenna ba tare da izini ba.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Yaushe suka aikata wannan sata a banki?

An gano wannan barnar ne lokacin da iyalan marigayin suka je bankin domin neman ragowar kudin da ke cikin asusun mamacin, Daily Nigerian ta ruwaito.

Iyalan sun nuna rashin amincewa da adadin kudin da bankin ya basu sannan suka aika da korafi ga bankin game da cirar kudi ba bias ka’ida ba a asusun mamacin.

Sakamakon wannan korafi, bankin ya gudanar da bincike na cikin gida, inda sakamakon ya bayyana cewa Ifah Ogoh, wanda ma’aikacin bankin ne, ya nemawa mamacin katin cire kudi a ranar 10 ga Mayu, 2023 kuma bankin ya amince bukatar.

Kara karanta wannan

Katsina: 'Yan bindiga sun turo saƙon bidiyon mutanen da suka sace a Maidabino

Bincike ya kai ga gano wadanda suka yi sata

Sakamakon bincike ya kuma nuna cewa Ogoh ya yi amfani da katin da kansa wajen cire kudin bayan hada baki da Agbo Okwute wanda shi ma ma’aikacin bankin ne wajen sace kudin.

Ana kuma zargin cewa, daga baya an cire kudaden ta hanyar hada baki da Agbo a lokuta daban-daban duk dai ba bisa ka’ida ba, rahoton Punch.

Za a gurfanar da wadanda ake zargin a gaban kotu da zarar an kammala bincike, kamar yadda rahotanni suka bayyana.

Yadda ma’aikacin banki ya saci kudin jama’a

A wani labarin, rundunar 'yan sandan jihar Ogun ta tabbatar da cewar Olumide Openaike, ma'aikacin bankin Kemta Oloko, wanda aka sanar da batansa da kuma gano shi a Mokwa, jihar Neja, shi ya kitsa garkuwa da kansa.

An sanar da hakan ne bayan gano cewa lamarin wani shiri ne da nufin dauke hankali daga bashin da ake Olumide na naira miliyan 1.7.

SP Omolola Odutola, kakakin 'yan sandan jihar, ya tabbatar da hakan ga manema labarai a ranar Talata, 30 ga watan Janairu.

Asali: Legit.ng

Authors:
Salisu Ibrahim avatar

Salisu Ibrahim (Head of Hausa Desk) Salisu holds BSc in IT (IOU, 2021) and is AfricaCheck's ambassador. He brings over five years of experience in writing, publishing and management. Trained by prestigious newspapers like Reuters, AFP, and Solutions Journalism Network, he curates news stories for the Hausa-speaking audience. He rose from Hausa Editor to Head of Desk at Legit. His commitment to excellence has earned him recognition, including the 2021 Best Hausa Editor award and the Legit Fearless Team Player of the Year 2023.