Bello Turji
Hadimin tsohon shugaban kasa Muhammadu Buhari, Bashir Ahmad ya bukaci a yi watsi da sulhu da Bello Turji ya ce zai yi da gwamnati. Ya bukaci a kashe dan ta'addan.
Yayin da ake yada batun cewa Bello Turji ya shirya ajiye makamansa, Sheikh Murtala Bello Asada ya samu damar tattaunawa da kasurgumin dan bindigar kan lamarin.
Sheikh Murtala Bello Asada ya sake yin tone-tone, ya soki masu fakewa da sulhu da ‘yan ta’adda, ya tabbatar da cewa an yaudare da karya yayin zama da yan bindiga.
Yaran dan ta'adda, Bello Turji sun kai hare hare jihar Sokoto. Sun kashe mutane da dama tare da sace wasu. Sojoji sujn ce har yanzu suna neman Turji ido rufe.
Wasu manoma a jihar Katsina sun koma gonaki cikin kwanciyar hankali, inda wasu suka ce shekaru da dama basu yi noma ba amma yanzu rayuwa ta sauya.
Malamin addinin musulunci, Musa Yusuf Asadus Sunnah ya hadu da hatsabibin dan bindiga Bello Turji domin tattauna batun sulhu. Hakan ya sanya ya sha suka sosai.
Sheikh Musa Yusuf Assadus Sunnah ya kalubalanci wasu malamai kan zargin da ake yi masa na zama da Bello Turji, inda ya ce yana aikin ne don maslahar al’umma ne.
Hedkwatar tsaro ta kasa (DHQ) ta yi magana kan rahotannin da ke cewa tantirin dan bindiga, Bello Turji, ya mika wuya. DHQ ta ce ana ci gaba da farautarsa.
Wasu 'yan bindiga da ke biyayya ga Bello Turji sun kai farmaki a Sokoto, inda suka kashe mutum daya, suka sace wasu 16, duk da batun sulhu da ubangidansu.
Bello Turji
Samu kari