Bello Turji
Kasurgumin dan ta'adda, Bello Turji ya fitar da sabon bidiyo inda ya ke gargadin lauya, Bulama Bukarti da kuma tura sako ga Isa Pantami da Murtala Bello Asada.
Gwamnan Sokoto, Ahmed Aliyu ya tanadi motoci 20 da babura 710 domin yakar yan 'ta'adda a jihar. Ana sa ran hakan zai kawo kashe Bello Turji da sauran yan ta'adda.
Cibiyar Centre Against Banditry and Terrorism (CABT) ta zargi Gwamna Dauda Lawal na Zamfara da hannu a ta'addanci da hakar ma'adinai ba ka'ida ba a jihar.
Gwamnatin jihar Sokoto ta ce Bello Turji a rikide ya ke saboda ganin shirin karar da su da Gwamna Ahmed Aliyu na jihar ya ke yi kan yaki da ta'addanci.
A wannan rahoton, za ku ji cewa Bidiyo wasu matasan sojoji guda uku ya dauki hankalin jama'a bayan an jiyo su suna gargadin kasungurmin dan ta'adda, Bello Turji.
A wannan labarin za ku ji cewa karamin Ministan tsaro, Dr. Bello Matawalle ya shiga gaba inda ya jagoranci hafsoshin tsaron kasar nan zuwa babban jihar Sakkwato.
Yayin da aka yada bidiyon tawagar Bello Turji suna kona motocin sojoji, malamin Musulunci, Sheikh Ahmed Gumi ya yi magana kan yadda rashin tsaro ya yi katutu.
A cikin wani bidiyo da aka wallafa, an gano dan ta'adda Bello Turji da yaransa suna shewa bayan samun iko da motocin sulke na sojoji guda biyu a daji.
Jami'an tsaro sun yi nasarar cafke wasu kasurguman yan bindiga da ke karkashin jagorancin rikakken dan ta'adda, Bello Turji a jihar Sokoto yayin wani samame.
Bello Turji
Samu kari