Bala Ngilari
Wasu Mutanen Jihar Bauchi sun je wawurar kayan tallafin COVID-19, sun sha kunya. Gwamna Bala Mohammed ya ce tuni ya kafa kwamitin da ya raba kayan ga mabukata.
A makon nan aka ji cewa Gwamnatin Bauchi ta kirkiro Hukumar BAROTA domin sa ido a kan tituna. Akwai makamanciyar wannan hukuma a irinsu Jihohin Kano da Kaduna.
A jiya Laraba ne Gwamnan Bauchi, Bala Mohd ya tabbatar da mutuwar mutanensa wurin ambaliya. Mummunar ambaliyar ruwa ta hallaka wasu Bayin Allah a Yankin Warji.
Bayan kusan watanni kimanin hudu, Mai dakin Mubarak Bala ba ta san inda Mijinta ya shige ba. Har Lauyansa yanzu wata da watanni kenan bai san inda ya ke ba.
Mun ji cewa a jiya ne Gwamnan Bauchi Bala Mohammed ya yi wa Yakubu Dogara raddi, ya ce Dogara ya tafi Jam’iyyar APC ne domin a share ta’adin da ya yi a NDDC.
A yayin da ake hira da gwamnan Bauchi, Bala Abdulkadir Mohammed kwanaki, tambayoyin wani ‘Dan jarida sun sa Gwamnan Bauchi ya harzuka ya yi fushi a gaban jama’a
Mun ji cewa Gwamnatin Bauchi ta koka game da adadin matan da ke mutuwa wajen zubar da ciki. Mata fiye da 200 sun mutu wajen kokarin zubar da juna biyu a Bauchi.
Sanata Bala Abdulkadir Mohammed ya bada umarni a biya Ma’aikatan Bauchi albashin Mayu. Gwamnatin Jihar Bauchi ta yi wannan ne domin a shirya bukukuwan Sallah.
Kullen da gwamnatin jihar Bauchi ta sa wa jama’a ya jawo magana sosai. Majalisar dokoki ta fito ta nuna ba ta goyon bayan haramta yin ibada a fili a Bauchi.
Bala Ngilari
Samu kari