Hadimina ya bude wa mutane dakuna, sun ga mun raba tallafi – Gwamnan Bauchi

Hadimina ya bude wa mutane dakuna, sun ga mun raba tallafi – Gwamnan Bauchi

- Gwamnan Bauchi ya ce ya raba wa masu bukata duk tallafin COVID-19 tun tuni

- Wannan ya sa tsagerun da su ka dura inda ake yin ajiya su ka yi zuwan banza

- Bala Mohammed ya ce tun a watan Mayu ya kafa kwamitin da ya raba kayan

Gwamnan Bauchi, Bala Mohammed, ya bada labarin yadda ta kaya tsakanin matasan jihar da shugaban ma’aikatan fadarsa, Ladan Salihu.

Wasu miyagu sun zo dakin adana na jihar Bauchi su na neman awon gaba da kayan tallafin COVID-19, amma ba su tashi da ko allura ba.

Gwamna Bala Mohammed ya yi bayani cewa a lokacin da Hadimin ya bude wa wadannan tsageru dakunan ajiyan, sun samu babu komai.

KU KARANTA: Buhari ya yi wa 'Yan Najeriya bayani bayan dogon kusufi

Bala Mohammed ya bayyana haka ne a shafinsa Twitter, ya ce tsagerun ba su ji dadin haka ba.

Sanata Mohammed ya ce tun tsakanin watan Mayu zuwa Agustan bana gwamnatinsa ta raba wadannan kaya na tallafin annobar COVID-19.

“Yau tsageru sun nemi su wawuri kayan tallafin COVID-19 a dakin adanan jihar Bauchi.” Inji sa,

“Aka sanar da shugaban ma’aikatan fadata, ya kuma bada umarnin a bude dakin ajiyar.”

“Sai su ka ga dakin wayam, su ka tafi. Saboda mun raba komai ga mabukata a lokacin da ya dace.”

KU KARANTA: Yaran wani ‘Dan Majalisa su ka yi hayar ‘Yan iska wajen zanga-zangar #EndSARS

Hadimina ya bude wa mutane dakuna, sun ga mun raba tallafi – Gwamnan Bauchi
Gwamnan Bauchi, Bala Mohammed Hoto: wikkitimes.com
Asali: UGC

“Domin ke-ke-da-ke-ke, lokacin da mu ka fara rabon kayan watannin da su ka wuce, na tabbatar an kafa kwamiti wanda na ke ciki (domin aikin).”

Gwamna ya bayyana cewa ainihin nauyin da ke kan sa shi ne ya tabbatar jihar Bauchi ta cigaba, ya kuma ce zai cigaba da kokarin ganin ya yi wannan.

A makon jiya kun ji cewa lamarin #EndSARS ya koyawa gwamnan jiha Enugu, David Umahi hankali har ta kai ya ba matasan kasar nan hakuri.

David Umahi ya roki Matasa su yi hakuri game da abubuwan da su ke faruwa a kasar.

Idan ku na da wata shawara ko bukatar bamu labari, tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Asali: Legit.ng

Authors:
Muhammad Malumfashi avatar

Muhammad Malumfashi (Hausa writer) M. Malumfashi ya samu Digirin farko a ilmin komfuta a ABU Zaria. Baya ga haka ya yi Digirgir a fannin kula da bayanai da wani Digirgir a ilmin aikin jarida duk daga jami'ar. Malumfashi ya kan kawo labaran siyasa, addini, wasanni da al’ada. Ya halarci taron karawa juna sani iri-iri. Imel: muhammad.malumfashi@corp.legit.ng