Umahi: APC ta na harin Ifeanyi Ugwuanyi, Ben Ayade da Bala Mohammed

Umahi: APC ta na harin Ifeanyi Ugwuanyi, Ben Ayade da Bala Mohammed

- Jam’iyyar APC ta na neman raba wasu Gwamnonin Jihohin adawa da PDP

- Ana rade-radin APC ta na zawarcin Gwamnonin Bauchi, Enugu da K/Riba

- Idan APC ta yi nasara, za ta sake samun karin jihohi uku daga hannun PDP

Jaridar This Day ta fitar da rahoto cewa jam’iyyar PDP mai hamayya ta na iya rasa wasu karin jihohi idan har APC ta samu yadda ta ke so.

Jam’iyyar APC ta na tattauna wa da wasu gwamnonin jihohin adawa bayan ta yi nasarar dauke gwamna David Umahi na Ebonyi daga PDP.

Yayin da jam’iyyar PDP ba ta gama makokin rasa gwamnan jihar Ebonyi ba, an samu labari cewa APC ta na hangen Kuros Riba, Enugu da Bauchi.

KU KARANTA: Gwamna Ortom ya fito ya yi magana game da rade-radin komawa APC

Rahotanni daga majiya mai karfi sun shaida cewa wakilan APC su na zama da Ifeanyi Ugwuanyi Ben Ayade da kuma gwamna Bala Mohammed.

Kawo yanzu an rasa gane abin da ya sa gwamnonin na Enugu, Kuros Riba da Bauchi su ke shakkar barin jam’iyyar da tayi masu riga da wando.

Majiyar ta shaida wa manema labarai cewa gwamnonin nan sun tabbatar da jajircewarsu, inda su ka fada wa jam’iyyar PDP ba za su sauya-sheka ba.

Gwamnonin sun yi magana ta bakin shugaban gwamnonin PDP, Aminu Waziri Tambuwal, bayan an kammala zaman NEC da aka shirya jiya a Abuja.

KU KARANTA: Barin PDP da na yi, bin Ubangiji ne - Umahi

Umahi: APC ta na harin Ifeanyi Ugwuanyi, Ben Ayade, da Bala Mohammed
PDP na harin Ben Ayade da Bala Mohammed
Asali: UGC

Shugaban jam’iyyar PDP na kasa, Prince Uche Secondus, shi ne ya jagoranci wannan zama da uwar jam’iyya ta kira bayan Dave Umahi ya koma APC.

Aminu Tambuwal a madadin gwamnonin jihohin hamayya 15, ya ce su na nan har gobe a PDP.

Kun ji cewa duka ‘Yan Majalisar Jihar Ebonyi sun bar Gwamna daga shi sai halinsa bayan ya koma APC mai mulki, sun ce su na nan a Jam’iyyar PDP.

‘Yan Majalisar Tarayya na jihar Ebonyi sun ce ba za su bi Dave Umahi, su shiga tafiyar APC ba.

Idan ku na da wata shawara ko bukatar bamu labari, tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Asali: Legit.ng

Online view pixel