Mutane fiye da 300 sun mutu a Bauchi a cikin kwanaki 14 – Mutanen Gari
Mazauna jihar Bauchi su na zargin wanzuwar mace-mace daga wani ciwo a garin Azare na karamar hukumar Katagum ta jihar.
A kalla mutum 301 suka rasa rayukansu a makonni biyu da su ka gabata a yankin, kamar yadda mazauna yankin su ka tabbatar. Wasu suna zargin ciwon da COVID-19.
A ranar Asabar da ta gabata gwamnatin jihar ta zargi jama'a da zuzuta lamarin.
Mataimakin gwamnan jihar, Baba Tela ya sanar da manema labarai cewa ana zuzuta lamarin da ke faruwa a Azare. Ya ce wadanda ba mazauna yankin ba na su ke yin wannan aiki.
Tsohon dan majalisar wakilai, Alhaji Ibrahim Baba, ya rubuta wasika ga shugaban kasa Muhammadu Buhari a ranar 8 ga watan Mayun 2020.
‘Dan siyasar ya yi magana a kan barkewar annobar Coronavirus a garin Azare na jihar. Ya ce an rasa rayuka sama da 100 sakamakon cutar a cikin mako daya.Wannan lamarin ya jefa zukata cikin rudani.
KU KARANTA: Za ayi bincike a kan Jihohi 2 da aka gaza samun cutar Coronavirus
Ya ce: "Na rubuto wasikar nan don janyo hankula a kan barkewar annobar Coronavirus a garin Azare da kewaye na jihar Bauchi, wanda a halin yanzu an samu mace-macen a kalla mutum 100 a cikin mako daya. Lamarin da ya jefe zukatan jama'a cikin dimuwa da rudani."
“Kusancin da ke tsakanin Bauchi, Kano, Azare da wasu manyan birane na jihar Jigawa ya sa aka fara zargin cutar coronavirus ce ta bulla a yankin.”
“Saboda kafafen yada labarai sun fi mayar da hankali a kan manyan birane, shiyasa ba su bada rahoton abubuwan da ke faruwa a Azare.”
Kamar yadda The Nation ta ruwaito, ya ci gaba da cewa: "Ina kira ga mai girma shugaban kasa da ya umarci NCDC da kwamitin shugaban kasa na yaki da cutar coronavirus da su hanzarta kawo dauki garin Azare.”
Ya kara da mika bukatar dakin gwaji ga shugaban kasar a jihar don samun damar yin aiki da shawo kan matsalar da gaggawa.
A wata wasika makamanciyarta da aka mika ga gwamna Bala Mohammed, Musa Azare ya yi ikirarin cewa an haka sabbin kaburbura 301 a makabartar garin cikin kwanaki 14 da su ka gabata.
Idan ku na da wata shawara ko bukatar bamu labari, tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng
Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu:
https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en
Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:
Facebook: https://facebook.com/legitnghausa
Twitter: https://twitter.com/legitnghausa
Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewa tare da mu.
Asali: Legit.ng