Majalisar Bauchi ba ta goyon bayan haramta taron ibada a Kananan hukumomi 3

Majalisar Bauchi ba ta goyon bayan haramta taron ibada a Kananan hukumomi 3

- Gwamnatin Bauchi ta hana fita a wasu manyan kananan hukumomi uku

- ‘Yan Majalisan Yankin sun nuna rashin goyon bayansu game da matakin

- Malaman lafiya sun ce za ayi fama da yawan haihuwar jarirai nan gaba

Jaridar The Guardian ta ce ba a tafiya a kan shafi guda tsakanin wasu ‘yan majalisar dokokin jihar Bauchi da kuma gwamnatin jihar a yunkurin da ake yi na yaki da cutar Coronavirus.

Rahotanni sun ce ‘yan majalisar sun tuburewa matakin da gwamnatin Bala Mohammed ta dauka na rufe duk dakunan ibada da ke cikin kananan hukumomin Katagum, Zaki da Giade.

Mai girma gwamna Bala Mohammed ya bada umarnin a rufe wuraren ibada domin a takaita yaduwar cutar COVID-19. ‘Yan majalisar Bauchi ba su gamsu da wannan mataki ba.

Shugaban masu rinjaye a majalisar dokokin Bauchi, Honarabul Aliyu Tijjani na jam’iyyar APC ne ya fara kawo batun a zauren majalisar a zaman da aka yi jiya, 13 ga watan Mayu, 2020.

KU KARANTA: Bala ya rufe wasu kananan hukumomi a Bauchi na tsawon kwanaki 10

Aliyu Tijjani mai wakiltar Azare da Madangala ya ce mutanen mazabarsa na Katagum sun fi kowa kamuwa da cutar, inda su ke da mutane 80 cikin 200 da su ka harbu da COVID-19.

Tijjani ya nuna cewa duk da haka babu bukatar gwamna ya garkame wuraren Ibadan jama’a. ‘Dan majalisar ya ke cewa akwai bukatar a samu hadin-kai tsakanin gwamna da majalisar.

Shi ma ‘dan majalisar Giade, Honarabul Dan’umma Bello ya nuna mamakinsa game da yadda aka halatta shiga kasuwanni a wasu ranukun, amma kuma ba za a bari a je wurin ibada ba.

Bello ya na ganin matakin da gwamna ya dauka na bada damar ayi zirga-zirga a ranakun Litinin, Laraba da Asabar, sannan kuma a rufe garuruwan a ranar Lahadi da Juma’a bai dace ba.

A wani gefe dabam, malaman asibiti sun koka kan karancin mutanen da ake samu wajen zuwa karbar maganin hana daukar ciki a dalilin takunkumin, wanda hakan zai jawo juna biyu.

Idan ku na da wata shawara ko bukatar bamu labari, tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewa tare da mu.

Asali: Legit.ng

Online view pixel