Bauchi: Mutane 5 sun rasu a sakamakon ambaliya a Karamar Hukumar Warji
Jaridar Guardian ta ce akalla mutane biyar aka rasa a wata ambaliya da ta barkowa wani yanki na karamar hukumar Warji, a jihar Bauchi.
Mai girma gwamnan jihar Bauchi, Sanata Bala Abdulqadir Mohammed, ya tabbatar da aukuwar wannan lamari, ya ce an rasa rai da dukiya masu yawa.
Bala Abdulqadir Mohammed ya shiga kauyen Dagu a ranar Alhamis, daya daga cikin inda ambaliyar ta faru, ya nuna takaicinsa a game da lamarin.
Bala Mohammed ya shaidawa al’ummar Dagu cewa gwamnatinsa ta damu da rayukan da ake rasawa da kuma dinbin dukiyar da ambaliyar ruwan ta cinye.
Kusan gidaje 300 ambaliyar ta yi wa barna, bayan haka an rasa dabbobi 2, 000 da amfanin gona.
Mai girma gwamnan ya gargadi mutanen wannan yanki da ake fama da ambaliya su daina tada gini a kan hanyar ruwa domin su gujewa wannan annoba.
KU KARANTA: Gwamna Ganduje ya shirya yaki da rashawa da rashin gaskiya
Jaridar ta rahoto cewa gwamnan ya bada kayan tallafin gaggawa ga wadanda su ka gamu da masifar. Kayan da aka raba sun hada da buhuna 100 na shinkafa da gero.
Bayan haka, gwamna Mohammed ya raba tufafi da tabarmi, sannan ya yi alkawarin bada wasu tallafin idan an gama bincike kan irin asarar da mutane su ka yi.
Gwamnatin Bala Mohammed ta ce kwanan nan za ta fara gina manyan hanyoyin ruwa da dakula da ruwa zai rika bi domin a gujewa aukuwar ambaliya nan gaba.
Shugaban hukumar BASEPA ta jihar Bauchi, Lurwanu Kabir, ya yi magana a kauyen, ya ce gwamnati ta ba su umarnin zagaye jihar domin duba halin da ake ciki.
Wannan kewaye da BASEPA za ta yi zai sa a san matakin da za a dauka tun wuri inji Kabir.
Idan ku na da wata shawara ko bukatar bamu labari, tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng
Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en
Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:
Facebook: https://facebook.com/legitnghausa
Twitter: https://twitter.com/legitnghausa
Asali: Legit.ng