Gwamna Bala Mohammed ya kafa Hukumar BAROTA a Jihar Bauchi

Gwamna Bala Mohammed ya kafa Hukumar BAROTA a Jihar Bauchi

- Gwamnatin Bauchi ta kirkiro Hukumar BAROTA domin sa ido a kan tituna

- Sanata Bala Abdulqadir Mohammed ya ce hukumar za ta rage hadura a jihar

- Akwai makamanciyar wannan hukumar a Jihohin Kano da kuma Kaduna

A cikin makon nan ne aka ji mai girma gwamnan jihar Bauchi, Bala Abdulqadir Mohammed, ya sa hannu a dokar da ta kirkiri sabuwar hukumar BAROTA.

Bala Abdulqadir Mohammed ya kawo wannan hukuma da za ta rika lura da abubuwan da su ka shafi kula da hanyoyi kamar yadda ake da su a wasu jihohi.

A lokacin da ya ke rattaba hannu a kan kudirin da ta kafa hukumar, gwamnan ya ce BAROTA za ta rika kula da hanyoyi da tabbatar da cewa ana bin dokar titi.

KU KARANTA: Bala ya bada umarnin a biya Ma'aikata albashi a Bauchi

Sanata Bala Abdulqadir Mohammed ya ce: “Hukumar (BAROTA) za ta gyara hanyoyinmu ta hanyar tabbatar da cewa duk masu bin titi sun bi doka a jihar.”

"Barin mutane su rika tuki a titi ba tare da doka ko hukuma da za ta sa ido wajen bin ka’ida ba, ganganci ne, kuma za a samu hadaura daga tukin wasu direbobi.”

Da ya ke jawabi, Gwamna Mohammed ya yi alkawari cewa zai nemi wasu kwararru da su ka san aiki da za su shugabancin wannan sabuwar hukuma da aka kirkiro.

Hukumar dillacin labarai ta rahoto gwamnan ya na wannan jawabi ne a ranar Laraba.

Gwamna Bala Mohammed ya kafa Hukumar BAROTA a Jihar Bauchi
Sanata Bala Mohammed
Asali: UGC

KU KARANTA: COVID-19 ta harbi Gwamnan Jihar Bauchi

Bayan haka, Bala Abdulqadir Mohammed ya bayyana cewa akwai kudirin kirkiro da hukumar SERMA da ya ke shirin kai wa gaban majalisar dokokin jihar Bauchi.

Wannan hukuma ta SERMA za ta rika gyara hanyoyin jihar Bauchi ne idan ta fara aiki.

Gwamnan ya yabawa ‘yan majalisar jihar Bauchi game da irin kokarin da su ke yi. Daga 2019 zuwa yanzu, majalisar ta shigo da kudirori 16 da yanzu sun zama dokoki.

Idan ba ku manta Gwamnan jihar Bauchi, Bala Mohammed, ya na cikin wadanda su ka kamu da Coronavirus a lokacin da cutar ta fara barkowa Najeriya a farkon bana.

Gwamnan ya killace kansa bayan ya kamu da cutar, a cewarsa wajen gaisawa da 'Dan Atiku Abubakar.

Idan ku na da wata shawara ko bukatar bamu labari, tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Asali: Legit.ng

Online view pixel