Bala Mohammed ya bada umarnin a biya Ma’aikatan Jihar Bauchi albashi

Bala Mohammed ya bada umarnin a biya Ma’aikatan Jihar Bauchi albashi

- Bala Mohammed ya bada umarni a biya Ma’aikatan Bauchi albashin Mayu

- Gwamnatin Jihar Bauchi ta yi wannan ne domin shirya bukukuwan Sallah

- Za a biya ma’aikatan gwamnatin jihar albashin nan da tsakiyar makon nan

Mai girma gwamnan jihar Bauchi, sanata Bala Abdulqadir Mohammed ya amince da biyan albashin ma’aikatan gwamnati na watan Mayun 2020.

Wani daga cikin hadiman gwamna Bala Mohammed, Muktar Gidado, ya bayyana cewa mai girma gwamna ya umarci a biya ma’aikatan jihar albashinsu.

Gwamna Mohammed ya umarci babban akawun gwamnatin jihar ya biya ma’aikata albashinsu na Mayu nan da ranar 20 ga watan nan na Mayun mai-ci.

Hakan na nufin da wannan umarni da gwamna ya bada, za a fara biyan ma’aikata daga yau Litinin, 18 ga watan Mayu zuwa ranar Laraba 20 ga wata.

KU KARANTA: Borno: Gwamna Zulum ya ce a biya ma'aikata albashin Mayu

Bala Mohammed ya bada umarnin a biya Ma’aikatan Jihar Bauchi albashi
Gwamna Bala Mohammed Hoto: Twitter
Asali: Twitter

“Gwamna ya dauki wannan mataki ne domin ma’aikata har da masu karbar fansho damar yin bukukuwan idin karamar sallah cikin jin dadi.” Inji Gidado.

“Gwamna Bala Mohammed ya tabbatarwa ma’aikatan gwamnati cewa gwamnatinsa za ta cika alkawarin da ta yi a biyan ma’aikata albashinsu kan kari.”

Mai taimakawa gwamnan wajen yada labarai ya ce bayan haka Mohammed zai cika alkawarin da ya yi na kawo gyara domin inganta aikin gwamnati a Bauchi.

A karshe mai girma gwamna ya yi kira ga jama’a su cigaba da bin duk dokokin da aka kafa domin takaita yaduwar annobar cutar Coronavirus a cikin jihar Bauchi.

Idan ku na da wata shawara ko bukatar bamu labari, tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewa tare da mu.

Asali: Legit.ng

Online view pixel