Dogara: Yunkurin rufe barnar da ka tafka ya sa ka koma APC – Bala Mohammed

Dogara: Yunkurin rufe barnar da ka tafka ya sa ka koma APC – Bala Mohammed

A ranar Litinin, gwamna Bala Mohammed na jihar Bauchi, ya yi magana game da sauyin siyasar da aka samu a PDP bayan Yakubu Dogara ya koma jam’iyyar APC.

Mai girma gwamnan na Bauchi ya ce Rt. Hon. Yakubu Dogara ya tsere daga jam’iyyar PDP zuwa APC ne domin tsoron bankado barnar da ya yi a ma’aikatar NDDC ta kasa.

Gwamna Bala Mohammed ya ke cewa ganin ana binciken badakalar da aka tafka a ma’aikatar da ke kula da Neja-Delta, ta sa Dogara ya sauya-sheka zuwa jam’iyya mai mulki.

A na sa bangaren, Yakubu Dogara ya fadawa mutanen mazabarsa cewa kishin kasa ta sa ya bar PDP, ganin irin salon mulkin da Bala Mohammed ya ke yi a jihar Bauchi.

Gwamnan ya maidawa tsohon shugaban majalisar wakilan kasar martani ta bakin wani Hadiminsa, Lawal Muazu Bauchi, wanda ya ce sam ba kishin kasa ta sa Dogara ya bar PDP ba.

KU KARANTA: Sunayen 'Yan Majalisar da aka ba kwagila a NDDC - Minista

Dogara: Yunkurin rufe barnar da ka tafka ya sa ka koma APC – Bala Mohammed
Gwamna Bala Mohammed
Asali: Twitter

Malam Lawal Muazu Bauchi ya ke cewa dalilan da Rt. Hon. Dogara ya bada na sauya-sheka ba za su iya gamsar da duk wani mai neman gaskiya ba.

“Ganin binciken da ake yi a majalisar tarayya game da badakalar kudi a ma’aikatar NDDC, mutum ba zai yi kuskure idan ya ce hanyar samun mafaka ga wadanda su ke da kashi a gindinsu shi ne su koma inda su ka fito ba.”

A game da zargin da Dogara ya ke yi wa gwamnatin PDP mai ci, Muazu Bauchi ya ce: “Gwamna Bala zai cika alkawarin da ya yi na shirya zaben kananan hukumomi ta sa ranar da za ayi wannan.

Ya ce: “Ana fitar da kashe-kashen kudin gwamnati a fili yadda kowa zai iya gani ba tare da boye-boye kamar yadda ake yi a baya ba, lokacin da ake wawurar biliyoyi ba tare da an yi wani aiki da za a gani ba.”

Hadimin Dogara, Turaki Hassan ya karyata wannan, ya ce shekara fiye da guda kenan da mai gidansa ya bar kujerar shugaban majalisa, kuma babu inda ake zarginsa da rashin gaskiya.

Idan ku na da wata shawara ko bukatar bamu labari, tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Asali: Legit.ng

Authors:
Muhammad Malumfashi avatar

Muhammad Malumfashi (Hausa writer) M. Malumfashi ya samu Digirin farko a ilmin komfuta a ABU Zaria. Baya ga haka ya yi Digirgir a fannin kula da bayanai da wani Digirgir a ilmin aikin jarida duk daga jami'ar. Malumfashi ya kan kawo labaran siyasa, addini, wasanni da al’ada. Ya halarci taron karawa juna sani iri-iri. Imel: muhammad.malumfashi@corp.legit.ng