‘Yan Sanda sun ki fada mani inda su ka kai Mai gidana – Uwargidar Mubarak Bala
A karshen watan Afrilu ne ‘yan sanda su ka cafke Mubarak Bala, yanzu kusan watanni hudu kenan ake nema ba tare da mai dakinsa, lauya ko ‘yanunwasa sun ji labarinsa ba.
Mai dakin wannan mutumi, ta yi hira da jaridar Punch, inda ta bayyana irin halin takaicin da ta ke ciki. A yanzu haka wannan Baiwar Allah ta na shayar da yaron da ta haifa kwanaki.
Ta ce: “Mu na zama ne a Abuja, na haifi jariri a farkon shekarar nan bayan an yi mani aiki, ina tsakiyar murmurewa ne maigidana ya ce mani zai yi tafiya zuwa garin Kaduna.”
Daga wannan tafiya da Mubarak Bala ya yi a ranar 28 ga watan Afrilu, ba a sake jin duriyarsa ba. “Sai dai kawai na ji an kama shi, washegari aka ce an wuce da shi zuwa garin Kano.”
Matar wannan Matashi ta ce yunkurin ji daga bakin kwamishinan ‘yan sanda ya ci tura.
‘Na samu lambar kwamishinan da ya sa aka kai shi Kano daga Kaduna, da na kira shi, sai ya fadi mani bai sanda inda mijina ya ke ba, ya yi mani magana maras dadi, ya kashe waya.”
Wannan mata ta nemi jami’an ‘yan sanda na reshen Kano da ke da alhakin tsare mijinta. “Na yi mamakin da na ji Mubarak ba ya hannunsu, su ka ce ba za su fada mani inda ya ke ba.”
KU KARANTA: Kotu ta daure Shugaban kamfanin man Rahamaniyyah da Yaronsa a Ingila
Mai dakin Bala ta ce kakakin ‘yan sanda na Kano ya fake da sunan sha’anin tsaro, ya ki bayyana mata inda aka kai mai gidanta, ta ce ‘yan sanda su na tsaron ta fadawa Duniya a kafofin sadarwa.
“‘Dan sandan ya ce ya na da faifen hirar da ya yi da mijina kuma zai aiko mani. Har yau bai kira ni ba. A ranar Litinin na aika masa sako ina rokonsa ya duba yanayin halin da na ke ciki.”
A wannan doguwar hira da aka yi da mai dakin mai sukar Islama, ta bayyana yadda aka hana har Lauyansa ya gana da shi. Ta ce ba za a iya gurfanar da Bala a kotu ba tare da Lauya ba.
“Na rubutawa Majalisa da sufetan ‘yan sanda takarda su sa baki. Rokona shi ne in samu in gan shi da ransa, ba ma a fito da shi ba tukun. Ina bukatar sanin ko mijina ya na da rai.” Inji ta.
Bala ya yi karatu a jami’ar Ahmadu Bello ta Zariya da kasar waje, yanzu haka jagora ne na wata kungiya ta masu da’awar babu Ubangiji, wanda wannan kira na sa ya jawo masa matsala.
Idan ku na da wata shawara ko bukatar bamu labari, tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng
Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en
Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:
Facebook: https://facebook.com/legitnghausa
Twitter: https://twitter.com/legitnghausa
Asali: Legit.ng