An koka game da adadin matan da ke mutuwa wajen zub-da-ciki a Jihar Bauchi

An koka game da adadin matan da ke mutuwa wajen zub-da-ciki a Jihar Bauchi

- Mata akalla 200 ake da labarin sun mutu a wajen zubar da ciki a Jihar Bauchi

- Gwamnati ta ce Likitocin da ba su san aiki ba ne su ke jawo wannan mace-mace

- Rilwanu Mohammad ya ce akwai bukatar wayar da kai game da sha’anin aure

Shugaban hukumar kula da matakin farko na kiwon lafiya a jihar Bauchi, Dr. Rilwanu Mohammad ya bayyana cewa mata fiye da 200 su ka rasa ransu sanadiyyar zub da ciki.

Dr. Rilwanu Mohammad ya ce wadannan mata sun mutu a sakamakon fadawa hannun ruba-ruban likitoci da malaman asibiti. Jaridar The Guardian ta fitar da wannan rahoto.

Rilwanu Mohammad ya yi wannan jawabi ne a ranar Juma’ar da ta gabata lokacin da ya ke tattaunawa da ‘ya ‘yan wata kungiya ta masana kiwon lafiya da ke jihar Bauchi.

Mohammed ya ce ana samun mace-mace ne a dalilin mata da su ke samun juna biyu ba tare da sun shirya ba, inda su kuma su ke tashi su fada hannun malaman da ba su kware ba.

KU KARANTA: An sallami jariri ‘dan wata 4 da haihuwa da ya ke jinya a Jihar Kaduna

An koka game da adadin matan da ke mutuwa wajen zub-da-ciki a Jihar Bauchi
Asibiti a Najeriya
Asali: UGC

Shugaban hukumar lafiya ta jihar ya ce kawo yanzu ba su karkare binciken da su ke yi ba, amma alamu sun nuna cewa adadin wadanda su ka mutu a Bauchi zai zarce haka yawa.

A cewar Dr. Mohammed, rashin isasshen ilmi game da harkar rayuwar aure da muhimmancin bada tazarar haihuwa ya ke jawo mata su ke karewa da daukar juna biyu babu shiri.

Akwai bukatar a wayar da kan ma’aurata game da zaman mata da miji a jihar Bauchi kamar yadda Dr. Mohammed ya bayyana a lokacin zantawarsa da wannan kungiya kwanaki.

Idan aka yi nasarar rage yawan juna biyu da ake samu, wannan zai taimaka wajen takaita adadin matan da ke rasa ransu a yunkurin zubar da ciki a hannun wadanda ba su san aiki ba.

A kwanakin baya jaridar fitar da rahoto cewa za a samu yawaitar mata masu ciki a Bauchi a sakamakon kafa dokar zaman gida da gwamnati ta yi saboda annobar Coronavirus.

Idan ku na da wata shawara ko bukatar bamu labari, tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Asali: Legit.ng

Online view pixel