Da taimakon David Mark aka nada ni Ministan Abuja a 2010 inji Bala Mohammed
- Bala Mohammed ya fadawa Duniya alherin da David Mark ya taba yi masa
- Gwamnan ya ce a dalilin Mark ne ya zama Minista a gwamnatin PDP a 2010
- Mohammed ya bayyana haka yayin da ya gayyaci 'Dan siyasar zuwa Bauchi
Gwamnan jihar Bauchi, Bala Mohammed, ya bayyana cewa taimakon David Mark ya na cikin abubuwan da su ka taimaka masa a harkar siyasa.
A ranar Laraba, 30 ga watan Disamba, 2020, jaridar Vanguard ta rahoto Sanata Bala Mohammed ya na yabon tsohon shugaban majalisar dattawan.
Bala Mohammed ya yabi Sanata David Mark ne jiya wajen kaddamar da aikin wasu tituna a Bauchi.
Mai girma gwamnan ya ce David Mark ya taka rawar gani wajen zamansa Ministan birnin tarayya Abuja, lokacin da siyasa ba ta yi da shi a Bauchi.
KU KARANTA: Gwamnan Bauchi ya musanya maganar ficewarsa daga PDP
Ya ce: “Mark ya bar tambari a tarihi na a lokacin da na ke Sanata da kuma Ministan babban birni.”
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
“Ba a zabe ni (Minista) a jiha ta ba, yin Ubangiji ne. Amma shi (David Mark) ya shiga, ya fita wajen ganin na zama Ministan babban birnin tarayya Abuja.”
“Lokacin da zan koma a karo na biyu, Mark ne ya yi tsayin-daka, ya ce dole sai Bala Mohammed ya koma kujerarsa, ban taba fadawa kowa wannan ba.”
Sanata Mohammed ya ce ya na ganin darajar David Mark a kan wannan alheri da ya yi masa, tare da godewa Ubangiji da ya ba shi damar zama Ministan.
KU KARANTA: An huro mani wuta in binciki Gwamnonin baya na - Bala
A na shi bangaren, tsohon Sanatan ya ce saboda irinsu Bala Mohammed ne ya kafa tarihin zama wanda ya fi dadewa a kan kujerar shugaban majalisa.
Kwanaki kun samu rahoto cewa gwamna Bala Mohammed na jihar Bauchi ya yi ikirarin cewa jam’iyyar PDP za ta dawo kan mulki a zabe mai zuwa.
Sanata Bala Mohammed ya ce mulkin Najeriya zai bar hannun shugaban kasa Muhammadu Buhari a 2023, ya kuma dawo hannun jam'iyyarsu ta PDP.
A wata hira da gwamnan ya yi da BBC, ya ce za su koma mulki ne dalilin rashin hadin kan 'yan APC.
Idan ku na da wata shawara ko bukatar bamu labari, tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng
Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en
Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:
Facebook: https://facebook.com/legitnghausa
Twitter: https://twitter.com/legitnghausa
Asali: Legit.ng