Gwamnan Jihar Bauchi Ya Bayyana Wanda Zai Lashe Zaben Shugaban Kasa a 2023

Gwamnan Jihar Bauchi Ya Bayyana Wanda Zai Lashe Zaben Shugaban Kasa a 2023

  • Gwamna Bala Abdulqadir Mohammed ya na sa ran Atiku Abubakar zai yi galaba a zaben shugaban kasa
  • ‘Dan takaran shugaban kasa ya kai ziyara zuwa Bauchi, inda ya karbi sababbin shiga jam’iyyar PDP
  • A jawabinsa, Gwamnan jihar Bauchi yace saboda Atiku Abubakar ne mutanen Bauchi suke barin APC

Bauchi - Mai girma gwamnan jihar Bauchi, Bala Abdulqadir Mohammed yace ‘dan takaran PDP, Atiku Abubakar ne zai lashe zabe mai zuwa na 2023.

Gwamna Bala Abdulqadir Mohammed ya yi alkawari idan Alhaji Atiku Abubakar ya karbi shugabancin Najeriya, zai hada-kan al’ummar kasar nan.

Mai girma gwamnan yace ‘dan takaransu zai jawo kowa a jikinsa, ba tare da nuna bamabanci ba. Daily Trust ta fitar da wannan rahoto a ranar Laraba.

Sanata Bala Mohammed ya yi wannan jawabi ne lokacin da ya karbi wasu da suka sauya-sheka daga sauran jam’iyyun siyasa, suka shigo jirginsu a PDP.

'Yan APC sun dawo PDP

Daga cikin wadanda aka karba a PDP a filin wasa na Abubakar Tafawa da ke garin Bauchi, akwai tsohon mataimakin gwamnan jihar, Abdu Sule Katagum.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Haka zalika shi ma shugaban majalisar dokokin Bauchi, Rt. Hon. Abubakar Suleiman ya shigo PDP.

Atiku Abubakar
Taron PDP a Bauchi Hoto: gwg.ng
Asali: UGC

‘Dan takaran shugaban kasar na jam’iyyar hamayyar, Wazirin Adamawa watau Atiku Abubakar ya halarci taron karbar tsofaffin ‘ya ‘yan na jam’iyyar APC.

Atiku zai ci zabe - Bala

“Mutanen jihar Bauchi suna son Atiku, kuma sun yarda da shi saboda sun san irin abin da zai iya, kuma mun shirya mara masa baya, mu ba shi kuri’u.
Muna tare da shi, kuma za mu yi masa aiki. Na san mafi yawan mutane suna shigo PDP ne ba don abin da muke yi ba, sai saboda ‘dan takararmu, Atiku.

“In sha Allahu, za kayi nasara a zaben shugaban kasa.”

- Bala A. Mohammed

Da ya tashi yin jawabi, an rahoto cewa Atiku ya yabi kokarin gwamnan na Bauchi, kuma ya karbi sababbin shiga PDP, yana kira ga mutane su zabi jam’iyyarsa.

This Day tace wadanda Atiku ya karba a jam'iyyar PDP sun kai mutum 140, 000.

An tsige Atare Awin

Dazu an ji labari wata hadimar kwamishinan ayyuka na jihar Delta, Atare Awin tayi magana a shafin Facebook, tana cewa Peter Obi yana da farin jini.

Ganin Gwamna Ifeanyi Okowa shi ne ‘Dan takaran Mataimakin Shugaban kasa a PDP, za su gwabza da Obi, sai aka sallami Awin daga kujerar da take kai.

Asali: Legit.ng

Online view pixel