Gwamna Bala ya yi wa ‘Dan jarida barazana wajen tattaunawa a gidan Gwamnati
Yayin da ake hira da gwamnan Bauchi, Bala Abdulkadir Mohammed bayan ya cika shekara guda kan mulki, gwamnan ya nuna wani ‘dan jarida da ‘dan yatsa, ya ce APC ya ke yi wa aiki.
Mai girma gwamnan jihar Bauchi ya yi wa ‘dan jaridar Daily Trust kaca-kaca a gaban sauran manema labarai. Hassan Ibrahim ya yi wata tambaya ne da ta batawa gwamnan jihar rai.
Gwamnan ya zargi wannan mai rahoto da cin amana, da aiki da jam’iyyar hamayya bayan da ya jefa masa tambaya game da zargin da ake yi masa na shake majalisar dokokin jihar Bauchi.
Yin wannan tambaya ke da wuya sai gwamnan ya maida martani cikin fushi: “Ka na tunani kai kadai ne ‘dan jarida. Na yi aikin jarida kafin ka!” Gwamnan ya yi aikin gidan jarida a baya.
Jaridar ta rahoto gwamnan ya na cewa: “Ka na nuna banbanci. Ka ma fitar da rahoto cewa mun yi watsi da wani mutumi a Alkaleri." Gwamna Bala ya fito ne daga karamar hukumar Alkaleri.
KU KARANTA: 'Yan adawa sun tasa ni a gaba tun da na hau mulki - Gwamna Bala
Gwamnan ya kara da: “Kullum ka na neman mugun abin da za ka fada ne a game da jihar Bauchi. Irin wannan rahoto bai da kyau. Ka rika kokarin yi wa abubuwa kallon alheri don Allah.”
“Ka na bakin kokarinka na ganin na yi fada da majalisata. APC sun saye ka, shi ya sa ka ke yin wannan aikin. APC ce ke da rinjaye a majalisa, ta ya ya zan hana ‘yan majalisa kudinsu?”
“Mutane sun ce ba su son tsohon gwamna Mohammed Abubakar, amma kai ka dage sai ka dawo da shi. Don Allah ku daina ruruta abubuwa, ku na jawo rikici a inda babu ita.”
“Idan tsohon gwamna ka ke yi wa aiki, zan sa ka daina aiki a jihar nan.” Inji gwamnan.
Kamar yadda ‘dan jaridar ya bada rahoto, gwamnan na PDP ya zarge shi da kokarin ci masa mutunci a daidai lokacin da gwamnatinsa ta ke bikin cika shekara guda ta na mulki a jihar.
Jaridar Daily Trust ta ce a karshe wasu jami’an tsaro sun fatattaki mai rahoton nan daga wurin da ake wannan taro.
Idan ku na da wata shawara ko bukatar bamu labari, tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng
Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu:
https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en
Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:
Facebook: https://facebook.com/legitnghausa
Twitter: https://twitter.com/legitnghausa
Asali: Legit.ng