Arewa
Yayin da mutane ke cikin wani hali na tsadar rayuwa, Gwamna Ahmed Aliyu na Sokoto ya ƙaddamar da “Shagon Sauki Na Amadun Alu” domin ma’aikata da 'yan fansho.
Rundunar yan sanda ta tabbatar da cewa wasu 'yan bindiga sun kashe shugaban PDP na mazabar Lade da dansa da wani mutumi a kauyen Mari, jihar Kwara.
Gwamnatin Adamawa ta ce sabuwar dokar masarautu ta shafi sarautar Atiku ta Wazirin Adamawa, amma mai magana da yawun gwamnan ya musanta cire shi.
Bayan Bello Turji ya gwabza da jami'an tsaro, gwamnatin Zamfara ta ce artabun da aka yi da ‘yan ta'adda ya zama gagarumar nasara wurin kisan yaran dan bindigar.
Gwamnan jihar Benue, Hyacinth Alia, ya fito ya yi Allah wadai da kisan wasu matasa suka yi wa matafiya 'yan Kano. Ya aika da sakon ta'aziyyarsa ga Gwamna Abba Kabir.
An yi rashi na daya daga cikin tsofaffin gwamnonin Najeriya. Cornelius Olatunji Adebayo wanda ya taba zama tsohon gwamnan jihar Kwara ya yi bankwana da duniya.
Wasu kungiyoyi a Arewa maso Gabas sun saba da juna kan wanda ya kamata a dauka a madadin Kashim Shettima a matsayin mataimakin shugaban kasa a zaben 2027.
Rundunar ƴan sanda ta bayyana cewa abin fashewa na UXO ne ya tarwatse a cikin kayan ƴan gwangwan a Kano, ba bam ba ne kamar yadda mutane ke yaɗawa.
Mutane biyu sun mutu a Kano saboda shakar guba a masai yayin da suke kokarin ciro waya. Wannan ba sabon abu bane; an taɓa samun irin wannan lamari a baya.
Arewa
Samu kari