Arewa
Daya daga cikin attajirai a duniya, Bill Gates ya ware gwamnatin jihar Gombe musamman domin yaba mata kan kawo sauyi a bangaren lafiya da sauran wurare.
Gwamnatin Adamawa ta ceto yara 14 da aka ceto aka sayar da su a jihar Adamawa zuwa jihar Anambra. Wata mata 'yar kabilar Ibo ake zargi da safarar yaran.
Rigima ta barke tsakanin wasu jagororin yan ta'adda a Katsina inda suka yi bata kashi yayin da ake maganar sulhu a yankuna da dama a jihar domin samun zaman lafiya.
'Yan bindiga dauke da makamai sun yi aika-aika bayan sun kai hare-haren ta'addanci a jihar Katsina. Sun hallaka mutane ta hanyar kona su da ransu.
Mutanen da suka tsira da ransu daga harin da 'yan bindiga suka kai cikin masallaci a jihar Katsina, sun yi bayanin yadda mummunan lamarin ya auku.
Yayin da ake yada batun cewa Bello Turji ya shirya ajiye makamansa, Sheikh Murtala Bello Asada ya samu damar tattaunawa da kasurgumin dan bindigar kan lamarin.
An yi jana'izar marigayi Alhaji Ahmed Momohsanni Ododo, mahaifin gwamnan jihar Kogi wanda Allah ya yiwa rasuwa ranar Litinin, manyan mutane sun halarta a Okene.
Gwamnatin jihar Benuwai ta mika sakon ta'aziyya ga iyalan marigayi mai ba gwamna shawara kan harkokin hulda da jama'a da siyasa, Mary Yisa, wacce ta rasu.
Hukumar NiMet ta sanar da cewa za a samu ruwan sama a jihohin Arewa a ranar Talata, yayin da ake sa ran samun yayyafi a wasu jihohin Kudancin Najeriya.
Arewa
Samu kari