'Dole Sai Gwauro': NDA Ta Fitar da Tsarin Dibar Dalibai Karo Na 76, Ta Bayyana Ka’idoji

'Dole Sai Gwauro': NDA Ta Fitar da Tsarin Dibar Dalibai Karo Na 76, Ta Bayyana Ka’idoji

  • Hukumar makarantar sojoji ta NDA ta fitar da sanarwar dibar dalibai da su ke da sha’awar shiga makarantar a karo na 76
  • Hukumar ta sanar da wannan bayani ne a yau Asabar 28 ga watan Oktoba a shafin Twiiter inda ta bayyana tsauraran ka’idoji
  • Ta bukaci masu sha’awar neman gurbin karatu a makarantar da su kasance gwauraye ne marasa mata ko dawainiya

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Abdullahi Abubakar, kwararren editan siyasa, kasuwanci da al'amuran yau da kullum ne, yana da gogewar aikin jarida sama da shekaru uku.

Jihar Kaduna – Rundunar sojin Najeriya ta sanar da daukar sabbin dalibai zuwa makarantar sojoji ta NDA kashi na 76.

Wannan na cikin wata sanarwa ce da rundunar ta wallafa a shafin Twitter a yau Asabar 28 ga watan Oktoba, Legit ta tattaro.

Kara karanta wannan

Da Dumi-Dumi: Jigon Jam’iyyar PDP a Najeriya Ta Riga Mu Gidan Gaskiya, Jam’iyyar Ta Shiga Dimuwa

Hukumar NDA ta fitar da jerin ka'idoji na cikewa don neman gurbin karatu
NDA Ta Fitar da Tsarin Dibar Dalibai Karo Na 76. Hoto: @NDefenceAcademy.
Asali: Twitter

Meye NDA ke cewa kan dibar sabbin dalibai?

Rundunar ta shawarci ma su sha’awar cike NDA da su guji biyewa ‘yan damfara wadanda ke yaudarsu inda ta bayar da ainihin yanar gizon da za a cika.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Sanarwar ta ce:

“Ku guji biyewa ‘yan damfara wadanda ke yaudarar mutane, ku duba wannan sashi don cika bayanan ku, http://nda.edu.g.”

Har ila yau, NDA ta bakin magatakardar makarantar inda ta bayyana wasu ka’idoji da za a bi kafin cika neman gurbin karatu a makarantar.

Wasu ka’idoji NDA ta fitar kafin cikewa?

Wadanda ke sha’awar cika NDA dole su kasance:

1. Ma su isashen lafiya da kuma halaye na gari.

2. Dole su kasance ba su da mata kuma ba su da wata dawainiyar yara a karkashinsu.

3. Su gabatar da satifiket na ainihin karamar hukumarsu ko jiha.

Kara karanta wannan

Da Dumi: Bayan Shan Kaye a Kotun Koli, Shugaban LP na Kasa Ya Sallami Hadimansa 5

4. Dole su kasance ma su shekaru 17 ko kasa da 21 zuwa watan Agusta na 2024.

5. Dole su ci darussa 5 a jarabawar gama sakandare da su ka hada da darasin Lissafi da Turanci.

6. Dole kuma su samu maki dai-dai yadda ake bukata a jarabawar JAMB.

7. Tsayinsu kada ya gaza mita 1.68 ga maza, mata kuma mita 1.65.

8. Ilimin yaren Faranci da Larabci ko Mandarin na da matukar muhimmanci.

An yaye dalibai 260 a jami'ar NDA

A wani labarin, hukumar makarantar NDA da ke jihar Kaduna ta yaye dalibai 260 bayan shafe shekaru shida.

Daliban da aka yaye sun hada da bangarorin soji da dama kamar Sojojin kasa, Mayakan Sama, da Sojojin ruwa.

Asali: Legit.ng

Online view pixel