Anambra
Jam'iyyar APC mai mulkin Najeriya ta ce ficewar Moghalu daga cikinta bai zo mata da mamaki ba saboda ta jima da gano shirinsa, ta masa fatan alheri.
Tsohon mai binciken kudi na kasa na jam'iyyar APC mai mulki a Najeriya, Cif George Moghalu, ya sanar da yin murabus daga jam'iyyar. Ya fadi dalilinsa.
A wani lamari mai ban tausayi, tsohon mataimakin kakakin majalisar dokokin jihar Anambra, Rt. Hon. Harford Oseke, ya yanke jiki ya mutu a wajen da ya ke motsa jiki.
'Yan bindigan da suka yi garkuwa da kwamishinan matasa na jihar Anambra tare da matarsa sun sako shi. 'Yan bindigan sun sako shi ne bayan ya yi kwana daya.
Wasu 'yan bindiga sun kai hari kan wani shingen binciken 'yan sanda a jihar Anambra. 'Yan bindigan sun hallaka jami'i daya a yayin harin da suka kai.
Rahotanni sun nuna cewa wasu ƴan bindiga sun yi garkuwa da mutane takwasa yayin da suka kai farmaki wurin bikin gargajiya a jihar Anambara da ke Kudu maso Gabas.
Ana fargabar wasu ƴan bindiga da ba a san ko su waye ba sun yi awon gaba da kwamishinan matasa na jihar Anambra tare da mai ɗakinsa ahanyar zuwa Abuja.
Kungiyar Miyetti Allah ta MACBAN ta nuna fargabarta yayin da ta ce akalla makiyaya 11 da shanu 33 ne aka nema aka rasa a jihar Anambra. Ta yi karin haske.
Rahotanni sun bayyana cewa yan bindiga sun kashe ɗan sanda yayin da suka tarwatsa wani abun fashewa a shingen binciken ababen hawa a jihar Anambra.
Anambra
Samu kari