Akwa Ibom
Rigima ta kaure tsakanin 'ya'yan tsohon gwamnan jihar Akwa Ibom, marigayi Idongesit Nkanga, yayin da 'ya'yan matarsa ta farko suka kai karar kishiyar mahaifiya.
An shiga jimami a cocin The Evening Church da ke a birnin Uyo na jihar Akwa Ibom, bayan mutuwar babban Faston cocin, Runcie Mike, wanda ya mutu ranar Asabar.
Wasu da ake zaton yan bindiga ne sun yi awon gaba da Eyo Edet, jigon jam’iyyar PDP kuma shugaban gidan man Eyotech Nigeria Limited, a jiharsa ta Akwa Ibom.
Godswill Akpabio, sabon shugaban Majalisar Dattawan Najeriya, ya nemi samun haɗin kan gwamnatin Shugaba Bola Tinubu, wajen tafiyar da ayyukansu cikin lumana.
Guiness World Record a karshe ta bayyana Hilda Baci a matsayin wacce ta kafa tarihi bayan ta shafe sa'o'i 93 ta na girki ba tare da hutawa ba a jihar Lagos.
An zaɓi Godswill Akpabio, a ranar Talata, 13 ga watan Yuni, a matsayin shugaban Majalisar Dattawan Najeriya ta 10, wacce sanatoci daga jam'iyyu daban-daban.
Musa Saidu ya ce Dattawan Arewa ba su tare da Godswill Akpabio domin Sanatan ba masoyin Arewa ba ne, hakan na zuwa ne bayan an ji wasu ‘Yan Arewa su na bayansa.
Dakarun hukumar yaki da cin hanci da rashawa EFCC sun kama wasu ɗaliban jami'ar jihar Akwa Ibom su 19 bisa zarginsu da hannu a aikata laifukan Intanet uku.
Gwamnan jihar Akwa Ibom, Udom Emmanuel, ya amince da naɗa wa mutane akalla 149 rawanin Dagaci a kauyukansu yayin da ya rage kwanaki 30 wa'adin mulkinsa ya kare.
Akwa Ibom
Samu kari