Aikin Hajji
An bayyana cewa manyan dalilan da suka janyo mahajjatan Najeriya suka sha fama da rashin lafiya, su ne cunkoso da aka samu a bana da kuma matsanancin zafin yan.
Hukumar alhazai ta jihar Kano ta sanar da rasuwar daya daga cikin maniyyatan jihar, Hadiza Isma'il a Makkah bayan fama da jinya a ranar Litinin 3 ga watan Yuli.
Hukumar alhazai ta ƙasa ta sanar da fara jigilar alhazan Najeriya na bana a ranar Talata 4 ga watan Yulin da muke ciki. An fara jigilar ne da alhazan Sokoto.
Gwamnan jihar Kano, Abba Kabir Yusuf wato gida-gida, ya bayar da kyautar kudi naira miliyan 65 domin a rabawa alhazan jihar 6,179 a matsayin barka da Sallah.
Gwamnan jihar Katsina, Malam Dikko Umaru Radɗa, ya bai wa alhazan jihar Katsina tallafin riyal 300 kowanensu kwatankwacin naira miliyan N278m a ƙasar Saudiyya.
Mercy Aigbe Adeoti, 'yar shirin fim a Najeriya ta wallafa faifan bidiyo tare da mijinta inda take nuna yadda Musulunci ya daidaita dukkan dan Adam a gaban Allah
Yayin da ake dab da fara jigilar alhazan Najeriya zuwa gida ranar Talata, 4 ga watan Yuli, Allah ya yi wa karin mutum biyu daga jihar Kaduna rasuwa a Makkah.
Alhazan Najeriya da suka gudanar da aikin Hajjin bana a ƙasa mai tsarki ta Saudiyya, za su fara dawowa gida Najeriya a ranar Talata, 4 ga watan Yulin 2023.
Gamayyar likitoci masu kula da alhazai sun ce mutane 13 ne suka mutu a aikin hajji, yayin da fiye da 40,000 suka kamu da rashin lafiya daban-daban a Saudiyya.
Aikin Hajji
Samu kari