Aikin Hajji
Kasar Saudiyya ta karrama Gwamnan Kano. An ware Gwamnan Kano an ba shi wata babbar kyauta. Wannan karramawa ta biyo bayan gamsuwa da kyakkyawan shirin Jihar Kano ne a aikin Hajji.
Wata kungiya mai zaman kanta dake kula da ayyukan Hajji da Umra ta duniya, Hajji and Umra Forum ta karrama gwamnan jahar Kano, Abdullahi Umar Ganduje sakamakon gamsuwa da tayi da kyakkyawan shirin da jahar Kano ta yi ma alhazanta
Bayan kammala aikin hajjin bana, gwamnan jihar Kano Abdullahi Umar Ganduje, ya aike da kyautar naira dubu biyar-biyar ga kowane daya daga cikin Alhazan Kano 3,170 dake kasa mai tsarki.
Shugaban majalisar ya bayyana hakan ne ga manema labarai a harabar filin jirgin saman kasa-da-kasa na Nnamdi Azikiwe dake Abuja, yayin dawowa daga kasar Saudiyya inda ya gudanar da aikin hajji a bana.
Rahotanni sun kawo cewa yawan adadin mahajjatan Najeriya wadanda suka mutu a kasa mai tsarki ya kai tara. Dr. Ibrahim Kana, Shugaban tawagar likitoci na hukumar kula da mahajjatan Najeriya (NAHCON), ne ya tabbatar da hakan.
Hukumomi a kasar Saudiyya sun sauya suturar dakin Ka’aba a ranar Asabar, 10 ga watan Agustan 2019. Duk shekara ana cire rigar sannan a maye gurbinta da sabuwa a ranar tara ga watan Dhu Al-Hijjah, wanda ya yi daidai da ranar Asaba
Gwamna Bala Muhammad na jihar Bauchi, ya ce shi da wasu mukarrabansa da suke aikin hajjin suna zaune ne a gidan alhazai na gama-gari daga jihar, maimakon kasaitaccen masauki ko otal.
Hukumar da ke kula da jin dadin Mahajjatan Najeriya (NAHCON) ta bayyana cewa maniyyatan kasar shida ne suka rasu a kasar Saudiyya.
Legit.ng ta ruwaito wannan mutumi da ba’a bayyana sunansa ba ya ciccibi mahaifiyarsa dattijuwa a wuyarsa, inda ya dinga zagayen Ka’aba dakin Allah da ita, ma’ana dai ya gudanar da dawafi dauke da mahaifiyarsa a wuyarsa.
Aikin Hajji
Samu kari