Gwamna Radda Ya Gwangwaje Alhazan Katsina da Kyautar Miliyan N278m

Gwamna Radda Ya Gwangwaje Alhazan Katsina da Kyautar Miliyan N278m

  • Gwamna Malam Dikko Umaru Raɗɗa ya bai wa alhazan jihar Katsina tallafin kuɗi miliyan N278m a Saudiyya
  • Shugaban tawagar alhajan bana, Alhaji Tasiu Musa-Maigari, ne ya tabbatar da haka a Makkah ranar Lahadi
  • Dikko Raɗɗa ya roki Alhazan su sanya jihar Katsina cikin addu'a, Allah ya kawo zaman lafiya mai ɗorewa

DUBA NAN: Bibiyi shafin Legit.ng Hausa a kafar TikTok. Kada ka bari bidiyo mai daukar hankali ya wuce ka!

Katsina - Gwamnan jihar Katsina, Malam Dikko Umaru Raɗɗa, ya raba wa alhazan jiharsa naira miliyan N278m kyauta a ƙasa mai tsarki.

Wannan na ƙunshe ne a wata sanarwa da sakataren watsa labaran gwamna, Malam Ibrahim Kaula ya rabawa manema labarai, kamar yadda The Nation ta ruwaito.

Gwamnan Katsina, Malam Dikko Radɗa.
Gwamna Radda Ya Gwangwaje Alhazan Katsina da Kyautar Miliyan N278m Hoto: Dr. Dikko Umaru Radda
Asali: Facebook

Sanarwan ta ce shugaban Alhazan jihar Katsina (Amirul Hajj), Alhaji Tasiu Musa-Maigari, shi ne ya tabbatar da haka a Makkah ranar Lahadi yayin da ya ziyarci alhazan.

Kara karanta wannan

Magana Ta Ƙare: Shugaba Tinubu Ya Ɗora Nauyin Dawo da Zaman Lafiya A Zamfara Kan Mutum 1

A rahoton hukumar dillancin labarai ta ƙasa (NAN), Musa-Maigari ya ƙara da cewa Malam Raɗɗa ya roki alhazan su yi addu'ar Allah ya kawo karshen matsalar tsaro a Katsina.

DUBA: Shigo shafin Legit.ng na manhajar Legit.ng na Telegram! Kada ka bari komai ya wuce ka

A cewarsa, mai girma gwamna ya umarce shi da ya miƙa sakon barka da sallah da taya murna ga Alhazan bisa kammala aikin Hajjin bana 2023 lafiya.

Gwamna Raɗɗa ya bai wa kowane Alhaji kyautar riyal 300

Daga ƙarshe, Musa-Maigari, tsohon kakakin majalisar dokokin Katsina ya sanar da cewa gwamna Raɗɗa ya bada tallafin Riyal 300 (kwatankwacin dubu N60,000) ga kowane Alhaji.

Ya ce gwamnan ya basu tallafin waɗan nan kuɗaɗen ne a matsayin alawus ɗin cin abinci gabanin su dawo gida Najeriya, kamar yadda Leadership ta ruwaito.

Tun da fari, shugaban hukumar jin daɗin alhazai ta jihar Katsina, Alhaji Suleiman Kuki, ya bayyana gamsuwa da kyawawan halaye da ɗabi'un da alhazan suka nuna a lokacin aikin hajjin bana.

Kara karanta wannan

Hajji 2023: Allah Ya Yi Wa Ƙarin Alhazan Najeriya 2 Rasuwa a Makkah Ana Shirin Dawowa Gida

Daga cikin waɗanda suka raka Amirul Ahajji zuwa wurin Alhazan sun haɗa da tsoffin mataimakan gwamna, Alhaji Abdullahi Garba-Faskari da Alhaji Abdullahi Garba Aminci.

Gwamnan Jigawa Ya Kai Ziyarar Ba Zata, Ya Kama Jami'an Lafiya Na Aikata Laifi

A wani rahoton na daban kuma Gwamna Umar Namadi na jihar Jigawa ya kai ziyarar ba zata babban Asibitin Dutse, babban birnin jiha ranar Litinin.

Yayin wannan ziyara, gwamnan ya tarad da malaman lafiya suna siyar da maganin da aka tanadar na kyauta ga kananan yara.

Asali: Legit.ng

Online view pixel