Jihar Adamawa
Wata sabuwar Soja a rundunar Sojan kasan Najeriya, Patience Amos Yau ta mutu a dakin saurayinta dake unguwar Damilu, cikin garin Jimeta a karamar hukumar Yola ta Arewa na jahar Adamawa.
Wasu gungun miyagu yan bindiga sun kaddamar da hari a gidan wani babban limamin coci Rabaran Denis Bagauri, wanda ake yi ma inkiya da Fasto Nyako, inda suka bindige shi har lahira.
Shugaban kwamitin majalisar dattawa kan rundunar soji, Ali Ndume, ya ce matsalar ta’addanci zai ci gaba a arewa maso gabas saboda rashin isassun kayayyaki da sojoji.
An shiga cikin wani tashin hankali bayan Boko Haram sun yi awon gaba da Shugaban CAN. Ana zargin ‘Yan Boko Haram ne su ka sace Shugaban Kiristoci a Jihar Adamawa.
Jami’an hukumar yaki da fasa kauri sun kaddamar da samame a kan cikin kasuwar Mubi inda suka kwace buhunan shinkafa yar kasar waje tare da sauran haramtattun kayayyakin da gwamnati ta hana cinikinsu.
Tattalin arzikin Najeriya ya dogara ne da kudaden shiga da gwamnati ke samu daga hada - hadar man fetur. Hakan yasa kasar ta dogara kacokan a kan tattalin arzikin man fetur tare da wofantar da sauran albarkatun da kasa keda su.
Uwargidar shugaban kasa, Aisha Buhari ta dauki biya ma dalibai 5000 yan asalin jahar Yola kudin zana jarabawar kammala sakandari ta WAEC da NECO, tare da daukan nauyin basu horo a kan yadda zasu fuskanci jarabawar.
Za ku ji cewa An budewa Yaron Atiku Abubakar sabuwar Ma’aikata a Jihar Adamawa a gwamnatin PDP. Yanzu za a ga yadda sababbin ma’aikatun za su taimakawa jihar.
Jiya ne Jam’iyyar PDP ta rabe gida 2, wasu ‘Yan taware sun bude R-PDP a Adamawa. Babban ‘dan siyasar nan Umar Ardo, ya ce ya jagoranci wannan tafiya ta taware ne saboda rashin bin ka’ida.
Jihar Adamawa
Samu kari