Adamawa: Adamu Atiku zai jagoranci sabuwar Ma’aikatar ayyuka

Adamawa: Adamu Atiku zai jagoranci sabuwar Ma’aikatar ayyuka

Gwamnan jihar Adamawa, Ahmadu Umaru Fintiri, ya nada ‘Dan cikin Alhaji Atiku Abubakar a matsayin Kwamishinansa. Atiku ne ya yi takarar shugaban kasa a PDP a zaben bana na 2019.

Adamu Atiku Abubakar ya na cikin Kwamishinonin Adamawa da su ka shiga ofis. Kwamishinoni 23 sabon gwamna Alhaji Ahmadu Fintiri ya nada bayan kusan watanni 6 da hawansa mulki.

Adamu Atiku shi ne zai jagoranci Ma’aikatar ayyuka da cigaban karfin wuta a gwamnatin jihar. A kan Atiku ne Gwamna Ahmadu Fintiri ya kafa wannan sabuwar ma’aikata a jihar Adamawa.

Sabon Kwamishinan, Alhaji Adamu Atiku Abubakar wanda ya fito daga Garin Jada, ya nuna cewa a shirye ya ke da ya shigo da irin na sa sababbin dabarun da za su kawowa jihar Adamawa cigaba.

Idan ba ku manta ba mutane biyu gwamna Fintiri ya zakulo a matsayin Kwamishinoninsa daga karamar hukumar Jada. Garin Jada ne Mahaifar tsohon mataimakin shugaban kasa, Atiku.

KU KARANTA: Mai dakin 'Dan takarar APC ta yi kuka bayan kotun koli ta hana ta zama Gwamna

Haka zalika gwamnan ya kafa wata sabuwar ma’aikata da za ta lura da aikin sake tada wuraren da rikici ya barke da su tare da bada agajin gaggawa da tallafi ga mutanen jihar Gabashin Arewan.

Mista Elijah Tumba shi ne zai jagoranci wannan sabuwar ma’aikata domin inganta rayuwar wadanda su ka gamu da ibtila’i a jihar. Elijah ya fito ne daga cikin karamar hukumar Machina.

Sauran Kwamishinonin da aka nada su ne: Usman Diyajo, Shuaibu Audu, Iliya James, Wulbina Jackson Sai Dishi Khobe da na-hannun daman Atiku; Umaru Daware da Ibrahim Mijinyawa

Haka zalika akwai irin su: Mohammed Umar, Ishaya John Dabari, Sunday Mathew, Hassan Kaigama , Umar Garba Pella, Lami Patrick, Abdullahi Prambe, Mustapha Jika da Adamu Titus.

Ragowar su ne: Bappa Dalhatu Isa, Aloysius Babadoke da kuma Justina Nkom. Jaridar The Sun ta ce jama’a za su zura idanu domin ganin yadda sababbin ma’aikatun za su taimakawa jihar.

Idan ku na da wata shawara ko bukatar bamu labari, tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewa tare da mu.

Ga masu bukatar manhajar mu na Musulunci sai a bibiyi wannan shafi

https://fb.gg/play/ramadan_ramadan

Asali: Legit.ng

Online view pixel