Mun karbi hukuncin kotun koli da zuciya daya – APC Adamawa

Mun karbi hukuncin kotun koli da zuciya daya – APC Adamawa

- Jam'iyyar APC reshen jihar Adamawa ta bayyana cewa ta amince da hukuncin kotun koli da zuciya daya

- Kotun koli ta tabbatar da zaben Gwamna Ahmadu Fintiri na jam’iyyar PDP a ranar Talata

- Jam'iyyar ta APC ta kuma yi godiya ga dukkanin wadanda suka mara mata baya a shari’arta har zuwa matakin kotun koli

Jam’iyyar All Progressives Congress (APC) reshen jihar Adamawa ta bayyana cewa ta amince da hukuncin kotun koli da zuciya daya.

Kotun kolin a ranar Talata ta tabbatar da zaben Gwamna Ahmadu Fintiri na jam’iyyar Peoples Democratic Party (PDP), ta kuma yi watsi da karar APC da dan takararta a zaben gwamnan da ya gabata, Mohammed Jibrilla Bindow, wanda ya kasance gwamna a lokacin da aka gudanar da zaben.

A wani jawabi daga sakatarenta, Mohammed Abdullahi, jam’iyyar ta taya tsohon gwamna Bindow, masu ruwa da tsaki, zababbun yan Majalisar wakilai, da masu yiwa jam’iyyar biyayya jaje a kan hukuncin kotun kolin, amma ta bukaci da su kwantar da hankalinsu.

KU KARANTA KUMA: Abdulmumin Jibrin ya saduda, yana neman sulhu da shugabannin APC gabannin zaben da za a sake (bidiyo)

Ya yi godiya ga dukkanin wadanda suka mara wa jam’iyyar baya a shari’arta har zuwa matakin kotun koli.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel