Jami’an Civil Defense sun kama muggan masu garkuwa da mutane 4 a Adamawa

Jami’an Civil Defense sun kama muggan masu garkuwa da mutane 4 a Adamawa

Hukumar tsaro ta farin kaya, Nigeria Security and Civil Defense Corps (NSCDC) ta sanar da samun nasarar cafke wasu gungun miyagun masu satar mutane, tare da garkuwa dasu har guda hudu a jahar Adamawa.

Gidan talabijin na Channels ta ruwaito kwamandan NSCDC reshen jahar Adamawa, Nurudeen Abdullahi ne ya bayyana haka yayin da yake bayyana miyagun mutanen ga manema labaru, ind yace sun kama su ne a garin Mubi bayan samun bayanan sirri game da ayyukansu.

KU KARANTA: Ba duka aka lalace ba: An karrama Dansandan da bai taba amsan cin hanci ba

Jami’an Civil Defense sun kama muggan masu garkuwa da mutane 4 a Adamawa
Jami’an Civil Defense sun kama muggan masu garkuwa da mutane 4 a Adamawa
Asali: Facebook

Kwamanda Nurudeen Abdullahi yace jami’an rundunar NSCDC tare da hadin gwiwar wata kungiyar sa kai ta kabilar Fulani, Pulako Tabitha ne suka kama miyagun da suka hada da; Ibrahim Usman, Musa Audu da Saidu Dahiru, a ranar 17 ga watan Janairu.

“Dukkaninsu sun amsa laifinsu na aikata laifn sata tare da garkuwa da mutane, a yanzu suna fuskantar bincike daga wajenmu, daga nan kuma zamu mikasu ga ofishin babban jami’I mai shigar da kara domin daukan matakin sharia a kansu.” Inji shi.

Guda daga cikinsu ya bayyana cewa a duk lokacin da suka saci mutum, shugabansu yana baiwa kowannensu N50,000, sa’annan da zarar sun kammala aikinsu zai amshe bindigunsu ya koma cikin kasar Kamaru inda yake buya.

“Gayyatarmu kawai ake yi idan za’a saci mutum, daga karshe sai a bamu N50,000. Bamu san nawa yake karba a matsayin kudin fansa ba, amma da zarar mun gama aikinmu zai kwace bindigunmu ya koma cikin Kamaru.” Inji shi.

Daga karshe kwamandan rundunar NSCDC na jahar Adamawa ya nemi jama’a dasu dinga basu bayanan sirri game da ayyukan miyagu a unguwanninsu, domin da haka ne kawai zasu iya kawo karshen ayyukan miyagu a al’umma.

Ku biyo mu a https://facebook.com/legitnghausa

ko a http://twitter.com/legitnghausa

KU LATSA: Hanyar sauko da sabuwar manhajar jaridar Legit.com Hausa cikin sauki

Ga masu shawara ko korafi, a same mu a labaranhausa@corp.legit.com

Sanarwa na musamman: Shafin NAIJ Hausa ya koma Legit Hausa

Asali: Legit.ng

Online view pixel