Arewa: Jihohi biyar da suka fi talauci a Najeriya da dalilin talaucinsu

Arewa: Jihohi biyar da suka fi talauci a Najeriya da dalilin talaucinsu

Najeriya kasa ce da Allah ya albarkata da ma'adanai masu daraja da suka hada man fetur, wanda shine ake ganin shine mafi muhimmanci.

Tattalin arzikin Najeriya ya dogara ne da kudaden shiga da gwamnati ke samu daga hada - hadar man fetur.

Hakan yasa tattalin arzikin kasa ya dogara kacokan a kan man fetur tare da wofantar da sauran albarkatun da kasa keda su.

Alkaluman da hukumar kididdiga ta kasa (NBS) ta fitar a shekarar 2015 sun bayyana cewa jihohin Najeriya da talauci ya yi wa katutu suna da mataki 70 zuwa sama a cikin 100 a mizanin auna talauci.

Ga jerin jihohi biyar ma fi talauci a Njeriya

1. Sokoto

Jihar Sokoto tana yankin arewa maso yamma. Yankin arewa maso yamma yana da Sahara da kuma tsananin zafin rana da wasu lokutan yake kai wa matakin 45C.

Mafi yawan mazauna jihar Sokoto, kaso 80%, sun dogara ne da noma kuma tana da kaso 80.2% a matakin talauci, lamarin da yasa ta zama jihar mafi fama da talauci a Najeriya.

2. Katsina

Jihar Katsina, kamar jihar Sokoto, tana yankin arewa maso yamma ne, kuma jama'ar jihar sun dogara ne da noma irin na duniyar da a matsayin hanyar dogaro da kai.

Hukumar NBS ta saka jihar Katsina a mataki na biyu a cikin jerin jihohi 5 da ke fama da talauci, kuma tana da kaso 74.5% a matakin talauci.

3. Adamawa

Sabanin jihohin Sokoto da Katsina, jihar Adamawa tana yankin arewa maso gabas kuma an kirkiri jihar ne daga tsohuwar jihar Gongola.

DUBA WANNAN: Jihohin Najeriya uku da suka ciri tuta a 'cin hanci' a shekarar 2019 - Kididdigar NBS

Alkaluman hukumar NBS sun nuna cewa jihar Adamawa tana da kaso 74.2% a matakin talauci, kuma ita ce jiha ta uku da ke fama da matsanancin talauci.

An alakanta karfin da talauci keda shi a jihar da al'amuran kungiyar Boko Haram da ke yawan kai hare - haren a sassan jihar da sauran jihohin yankin.

4. Gombe

Kamar jihar Adamawa, jihar Gombe tana yankin arewa maso gabas, kuma an fitar da ita ne daga jihar Bauchi. Ta kasance a mataki na hudu a jerin jihohin dake fama da talauci da kaso 74.2%, a cewar hukumar NBS.

Duk da kasancewar an gano wasu ma'adanai a jihar, har yanzu mafi yawan jama'ar jihar sun dogara ne da noma.

5. Jigawa

An kirkiri jihar Jigawa ne daga jihar Kano a shekarar 1991, kuma tana yanki daya da jihohin Sokoto da Katsina.

Hukumar NBS ta bayyana cewa jihar Jigawa tana da kaso 74.1% a matakin talauci, kuma mafi yawan jama'ar jihar sun dogara ne da noma a matsayin sana'ar dogaro da kai.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel