Jami’an kwastam sun kai samame kasuwar Mubi, sun tattara buhunan shinkafar waje

Jami’an kwastam sun kai samame kasuwar Mubi, sun tattara buhunan shinkafar waje

Jami’an hukumar yaki da fasa kauri sun kaddamar da samame a kan cikin kasuwar Mubi inda suka kwace buhunan shinkafa yar kasar waje tare da sauran haramtattun kayayyakin da gwamnati ta hana cinikinsu.

Rahoton kamfanin dillancin labarun Najeriya, NAN, ta ruwaito babban kwamandan hukumar na shiyyar Aadmawa/Taraba, Kamardeen Olumoh ne ya jagoranci samamen zuwa kasuwar, inda suka samu nasarar kama buhunan shinkafa da dama tare da mutane uku.

KU KARANTA: Sata ta saci sata: Masu garkuwa da mutane sun kashe jagoransu bayan ya tsere da naira miliyan 5

Majiyar Legit.ng ta ruwaito yan bindigan tare da taimakon jami’an rundunar Yansandan Najeriya sun kaddamar da samamen ne da misalin karfe 11 an safiyar Juma’a inda suka kutsa kai cikin shaguna da sito sito na ajiyan kayayyaki.

A jawabinsa, kwamanda Kamardeen ya bayyana cewa sun kaddamar da samamen ne bisa umarnin babban kwanturolan hukumar yaki da fasa kauri, Kanal Hamid Ali mai ritaya.

“Matsalar safarar haramtattun kaya a yankin nan yana kara hauhawa, don haka babban kwanturolan kwastam ya bamu umarnin shiga kasuwar Mubi domin tabbatar da an tsaftace ta daga dukkanin haramtattun kayan fasa kauri, musamman shinkafar waje.

“A yau dai mun shiga kasuwar, kuma mun samu nasarar kama shinkaga mai tarin yawa, wannan ya zama kashedi ga masu fasa kauri, doka ce ta bamu daman yin hakan, sashi na 147 ya bamu daman mu yi bincike ko da dare ko da rana, tare da kama duk wani mai laifi.” Inji shi.

Sai dai wannan samame ya kawo rarrabuwar ra’ayi tsakanin jama’a a garin Mubi, yayin da yan kasuwa suka yi tir da shi, su kuwa manoma maraba suka yi da shi tare da bayyana farin cikinsu a kan hakan domin sun ce hakan zai kawo habaka wajen kasuwancin shinkafar gida.

Ku biyo mu a https://facebook.com/legitnghausa

ko a http://twitter.com/legitnghausa

KU LATSA: Hanyar sauko da sabuwar manhajar jaridar Legit.com Hausa cikin sauki

Ga masu shawara ko korafi, a same mu a labaranhausa@corp.legit.com

Sanarwa na musamman: Shafin NAIJ Hausa ya koma Legit Hausa

Asali: Legit.ng

Online view pixel