Aisha Buhari ta dauki nauyin biyan kudin WAEC da NECO ga dalibai 5000 a Adamawa

Aisha Buhari ta dauki nauyin biyan kudin WAEC da NECO ga dalibai 5000 a Adamawa

Uwargidar shugaban kasa, Aisha Buhari ta dauki biya ma dalibai 5000 yan asalin jahar Yola kudin zana jarabawar kammala sakandari ta WAEC da NECO, tare da daukan nauyin basu horo a kan yadda zasu fuskanci jarabawar.

Aisha ta dauki nauyin wannan hidima ne a karkashin gidauniyarta ta Future Assured, inda kamar yadda jami’I mai kula da gidauniyar a jahar Adamawa, Yau Babayi ya bayyana a yayin taron yaye mata da maatsa 600 da suka samu horo a sana’o’I daban daban.

KU KARANTA: Gwamna Nasir El-Rufai ya rattafa hannu kan kasafin kudin 2020 na jahar Kaduna

Babayi yace manufar gidauniyar shi ne tallafa ma mata da matasa a fadin jahar Yola, don haka suka zabo matasa marasa galihu daga kananan hukumomi 21 na jahar Adamawa domin su ci gajiyar biyan kudin jarabawar WAEC da NECO, daga nan kuma su cigaba da karatunsu.

“A karkashin Future Assured, an dauki yara 5,000 wanda a yanzu haka suna samun horo a wasu darussan karatun boko domin su shirya ma jarabawar WAEC da NECO yadda ya kamata, wanda gidauniyar za ta biya musu.

“Zamu gudanar da horon a shiyyoyin sanatoriya guda uku na jahar; za’a yi horon a jami’ar jahar Adamawa dake Mubi a shiyyar sanatoriya ta Arewa, a sanatoriya ta tsakiya kuwa za’a yi ne a kwalejin Aliyu Musadafa Yola da yayin da daliban shiyyar kudancin jahar zasu yi nasu a kwalejin noma dake Ganye.” In ji shi.

Wasu daga cikin wadanda suka amfana da tsarin, Dinatu Wakawa da Bilkisu Usman sun jinjina ma uwargidar shugaban kasa tare da bayyana godiyarsu a gareta.

A wani labarin kuma, gwamnatin tarayya ta bayyana cewa ta bankado wasu manyan malaman jami’o’in Najeriya guda 100 masu darajar karatu ta Farfesa amma fa ta bogi, kamar yadda shugaban hukumar kula da jami’o’in Najeriya, NUC, ya bayyana.

Ku biyo mu a https://facebook.com/legitnghausa

ko a http://twitter.com/legitnghausa

KU LATSA: Hanyar sauko da sabuwar manhajar jaridar Legit.com Hausa cikin sauki

Ga masu shawara ko korafi, a same mu a labaranhausa@corp.legit.com

Sanarwa na musamman: Shafin NAIJ Hausa ya koma Legit Hausa

Source: Legit

Online view pixel